JUZU’I NA BIYU NA RATAYE
NAVIGATION
136. Page
JUZU’I NA BIYU NA RATAYE
Wanda shi “Maƙamomi tara ne”game da matakai tara na hujjojin tashin Alƙiyamasu ne waɗanda ayoyi masu zuwa suka yi nuni zuwa gare su nuni na mu’ujiza.
Matsayi na farko:
فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمۡسُونَوَحِينَ تُصۡبِحُونَ * وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِوَعَشِيّٗا وَحِينَ تُظۡهِرُونَ * يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَيُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ[1]
Da sannu za a bayyana kuma a yi bayani dalla-dalla in sha Allahu game da abin da waɗannan ayoyi suka bayyana na dalili mai matuƙar ƙayatarwa da hujja mai yanke shakku game da lamarin tashin Alƙiyama[2].
Haƙiƙa an bayyana a cikin “Keɓanta ta Ashirin da Huɗu” daga batun “Rayuwa” cewa rayuwa tana fuskantuwa zuwa rukunan imani guda shida kuma tana tabbatar da su, kuma tana nuni zuwa tabbatarsu[3].
Na’am; tun da dai cewa mafi muhimmancin sakamakon wannan halitta da asalinta da haƙiƙaninta da hikimar halittarta ita ce rayuwa; to ba makawa cewa ita waccan haƙiƙa maɗaukakiya ba ta taƙaita a cikin wannan rayuwa ta duniya mai ƙarewa gajeriya tauyayyiya mai raɗaɗi kuma ba ta tuƙewa gare ta, maimakon haka ma haƙiƙa manufa da sakamakon bishiyar rayuwa wadda ke fahimtar da girman haƙiƙaninta da keɓance-keɓancen rayuwa guda ashirin da tara, da ‘ɗan itaciya mai dacewa da girman waccan bishiya ita ce rayuwa ta har abada madawwamiya, da rayuwar Lahira, da rayuwa a gidan rabauta wadda ita ce ainihin rayuwa da duwatsunta da bishiyoyinta da turɓayarta, in ko ba haka ba to sai ya zamo lallai bishiyar rayuwa da aka yi wa tanadi da sassan jiki masu aiki masu muhimmanci da ba su da iyaka ta wanzu ba tare da amfani ko fa’ida ba, ko wata haƙiƙa ga ma’abocin ji a jiki musamman ma bil Adama, kuma da sannu za ta sarayo da bil Adaman wanda shi ne mafi girman abin halitta a cikin halittukuma a tsakanin ma’abota rayuwa kuma mafi ɗaukakarsu mafi muhimmancinsu zai zama ya
[1]{Saboda haka tsarkakewa ta tabbabta ga Allah a lokacin da kuke shiga maraice da lokacin da kuke shiga safiya. Kuma godiya tasa ce a cikin sammai da ƙasa da lokacin yammaci da lokacin zawali.Yana fitar da mai rai daga matacce, kuma yana fitar da matacce daga mai rai, kuma yana rayar da ƙasa bayan mutuwarta,kuma kamar haka ake fitar daku (daga ƙaburburanku)}[Ar-Rum:17-19].
[2] Ba a rubuta wannan matsayar ba tukunna, domin an shigar da batun rayuwa a nan saboda alaƙarta da tashin Alƙiyama, sai dai nuni rayuwa a ƙarshensa zuwa rukunin ƙaddara ɓoyayyiya ƙwarai kuma mai zurfi ƙwarai ba kowa ne zai gane ta ba, kuma tun da ‘yan’uwa sun rubuta ta ni ban taɓa ta da komai ba don ta wanzu.(mawallafi).
[3] Za a yi bayanin haka dalla-dalla cikin “sirrin hikima na biyar”wanda aka keɓance don sharhin sunan Allah na “Rayayye” daga “Haske na talatin” daga littafin “Hasake”.(Mawallafi).
137. Page
gangaro matakala ashirin ƙasa da tsuntsu ta ɓangaren farin ciki da rabauta ta rayuwa, tare da cewa shi ya fishi ɗaukaka da daraja ashirin-bisa misali-ta ɓangaran jari da kayan aiki (sassan jiki masu aiki), kuma zai zama halitta mafi taɓewa da ƙasƙanci da gazawa, kuma hankalin da yake mafi girman ni’ima kuma mafi tsadarta zai zamo musiba mafi girma, da bala’i mafi tsanani ga mutum mai azabtar da zuciyarsa na har abada, kuma mai gurɓata jin daɗinsa guda ɗaya da raɗaɗi tara, ta hanyar yin tunani cikin baƙƙan cikin lokacin da ya wuce da tsorace-tsoracen lokaci mai zuwa, wannan kuwa ƙarya ce da mataki ɗari,kenan haƙiƙa rayuwar duniya tana tabbatar da rukunin imani da Lahira tabbatarwa mai yanke shakku,kuma a kowane lokacin kaka tana nunawa idanunmu fiye da samfuri dubu ɗari uku na tashin Alƙiyama, to ya jama’a, shin mai yiwuwa ne ga mai tasarrufi mai iko wanda yake tanadar dukkan abubuwa da sassan jiki da ake matuƙar buƙata da suka dace da rayuwarka a cikin jikinka da lambunka da mazauninka cikin hikima da kulawa, kuma ya sadar da su a lokacinsu, har ta kai Shi yana sani kuma yana jin addu’a makeɓanciya ta ɓangare daga tumbinka ta neman azurtawa don kwaɗayin wanzuwa da rayuwa, kuma yana bayyana amsawarSa ga addu’arsa da abinci masu daɗi da ba su da iyaka, kuma yana yardar da shi? Shin mai yiwuwa ne ga wannan mai tasrifin mai iko a ce bai san ka ba kuma ba ya ganinka, kuma ba ya tanadin sababai na tilas ga rayuwa ta har abada wadda ita ce mafi girman manufa ta nau’in jinsin bil Adama, kuma a ce ba zai amsa mafi girman addu’ar bil Adama, kuma mafi muhimmancinta kuma mafi cancantarta ba, kuma mafi gamewarta ba, wadda ita ce wanzuwa ta har abada ta hanyar samar da rayuwar Lahira da samar da aljanna, kuma a ce ba zai ji addu’a magamiya mai ƙarfi wadda ta girgiza Al’Ar’arshi da Shimfiɗar duniya ta mutum wanda shi ne mafi muhimmancin abin halitta cikin halittar, kuma sarkin ƙasa kuma sakamakonta ba, kuma a ce ba zai ba shi muhimmanci ba, kuma ba zai yardar da shi ba kamar yadda yake yi wa tumbi ƙarami, sai wannan ya janyo inkarin kamalar hikimarSa da rahamarSa cikakkiya?Tsarki ya tabbata gare shi sau dubu ɗari Tsarki ya tabbata gare shi.
138. Page
Sannan kuma shin abu ne mai yiwuwaya ji muryar mafi ɓoyuwar sautin mafi ƙanƙantar abu a rayuwa kuma Ya ji kokensa kuma ya warkar da shi, ya yi masa mu’amala da tausasawa, ya amsa dukkan burace-buracensa da buƙatunsa, ya raine shi da cikakkiyar kulawa da himmatuwa ya hore komai domin hidimta masa cikin tantancewa da damuwa da kulawa, ya hore masa ababan halittarsa manya, kuma a ce ba zai ji mafi ɗagawar sauti da ya yi kama da rugugin tsawa na mafi girman rayuwa kuma mafi tsadarta mafi dawwamarta mafi taushinta ba, kuma a ce ba zai himmatu da addu’arsa muhimmiya ƙwarai ta neman wanzuwa ba, kuma ba zai kula da kamun ƙafarsa da addu’arsa da ahinsa ba? Kuma misalinsa ya zama kamar misalin wanda yake kintsa wani soja kuma yake sarrafa shi cikin cikakkiyar himmatuwa, amma a ce ba zai kalli kuma ya damu da wata runduna mai girma mai biyayya ba, kuma yana ganin ƙwayar zarra amma ba ya ganin rana, kuma yana jin zazun ƙuda amma ba ya jin rugugin tsawa ? tsarki ya tabbata a gare shi sau dubu Tsarki ya tabbata a gare shi.
139. Page
To shin hankali ta kowace fuska daga fuskoki zai karɓi cewaالقديرMai iko الحكيمMai hikima ma’abocin jin ƙai na sake babu ƙaidi da so mara iyaka da tausayi mara iyaka, kuma wanda yake son ababan samarwarSa daƙirƙirarSa so mai yawan gaske, kuma yake sanya soyayyar kanSa sanya soyayya mai yawa, kuma yake son masu sonSa so mai yawa; muna cewa:Shin abu ne mai yiwuwa ya ƙarar da rayuwa abar so abar ƙauna wadda ta ke son mai iko mai hikima so mai tsanani fiye da duk wani abin halitta daban, kuma wadda ta ke son mahaliccinta da gundarin ɗabi’ar halittarta, kuma a ce ya ƙarar da ruhin da shi ne rayuwa da haƙiƙaninta ta hanyar rasarwa da mutuwa ta har abada, kuma ya munanawa mai sonSa kuma masoyinSa munanawa ta har abada, kuma ya sanya shi mai jin haushinSa ne, kuma ya sanya masa raɗaɗi raɗaɗi mai tsanani, sai ya yi inkarin sirrin jin ƙanSa da hasken sonSa kuma ya sabbaba inkarinsu? Tsarki ya tabbata a gare shi sau dubu ɗari Tsarki ya tabbata a gagreShi! Don haka babu shakka kuma babu kokwanto cewa kyawu cikakke wandaya ƙayata wannan halitta da tajallolinsa, da rahama ta sake babu ƙaidi wadda ta ke ƙayatarda dukkan ababan halitta ababan tsarkakewa ne ba tare da iyaka ba daga irin wannan lamari mai muzantawa, da kuma wannan munin da zaluncin na sake babu ƙaidi daga kuma tsaurarawa.
140. Page
Sakamako:Tunda dai cewa a cikin duniya akwai rayuwa; to babu shakka cewa waɗanda suke fahimtar sirrin rayuwa daga cikin mutane kuma ba sa munana amfani da rayuwarsu za su sami rayuwa wanzajjiya a gidan wanzuwa da Aljanna wanzajjiya, mun ba da gaskiya da haka.
Sannan kuma kamar yadda ƙyalƙyalin abubuwa masu ƙyalli a kan doron ƙasa yake kasancewa dalilin haskawar rana ne, kuma ƙyalƙyalin abin da ke kan fuskar ruwa na daga ƙwaiƙwayen ruwa da kumfarsa suna kasancewa ne da haskawar haske da kuma bucewarsa, kuma kasancewarsu suna yin aiki irin na madubi saboda abin da yake bibiyar juna a kanta na daga ƙwai-ƙwayen ruwa da kumfa da ‘yan rana-rana da hankali ke surantawa, duk wannan yana nuni kamar yadda kowa ya sani a kan cewa waɗancan haskake-haskaken ba komai ba ne face haskuwa ta tajallolinn rana guda ɗaya mai ɗaukakuwa, kuma cewa su suna tuna mana samuwar rana da harasansu mabambanta, kuma suna nuni zuwa gare ta da ‘yan yatsunsu na haske, to hakanan ma ƙyalƙyalin a bin da yake kan fuskar tsandauri da abin da yake cikin kogi na abu mai rai da tajalli mai girma na sunan mai rayawa na rayayye tsayayye da zatinSa, da kuma iko na Allahntaka, sannan kuma ɓuyansu a bayan labulen gaibi suna masu cewa يا حيYa rayayye ; domin dai su ba da guri ga abin da zai zo bayansu domin shi ma ya ba da shaida bisa rayuwar ma’abocin rayuwa ta har
141. Page
abada da wajabcin samuwarSa, kuma ya yi nuni zuwa gare ta da isharori, hakanan dukkan dalilai da suke shaidawa bisa ilimin ubangijintaka wanda gurabansa suke bayyyana cikin tsara dukkan samammu, da dukkan hujjoji da suke tabbatar da iko mai tasarrufi a cikin halitta, da dukkan hujjojin da suke tabbatar da nufi da so waɗanda suke mamaye tsara halitta da gudanar da ita, da alamomi da mu’ujizozi waɗanda suke tabbatar da manzanci wanda a kansa ne zancen ubangijintaka da wahayi na Allahntaka ke gewayawa, hakanan dukkan dalilai da suke shaidawa bisa siffofin Allahntaka guda bakwai suna nuni bisa rayuwar rayayye mai tsayuwa da zatinsa, kuma suna shaidawa da su, kuma suna nuni zuwa gare su;domin idan akwai gani cikin abu to tabbas akwai rayuwa a cikinsa kuma,hakanan idan yana da ji to wannan alamar rayuwa ce, idan yana da zance to hakan na nuni zuwa samuwar rayuwa, idan kuma yana da zaɓi da nufi to waɗannan suna nuni zuwa rayuwa, hakanan duk abin da sananne ne samuwarsa kuma tabbatacci ce da gurabunsa a halitta na daga ƙudura ta sake babu ƙaidi,da nufi gamamme da sani mai kewayewa da makamantansu na daga siffofi, duka suna shaidawa da dukkan dalilansu bisa rayuwar rayayye mai tsayuwa da zatinSa da kuma wajabcin samuwarSa, kuma suna shaidawa bisa rayuwarSa ta har abada wadda ta ke haskaka halitta dukkaninta da wata inuwa daga inuwoyinta, kuma ta ke tado da rayuwa saboda gidan Lahira tare da ƙwayoyin zarrarta gaba ɗaya da tajalli daga tajallolinSa.
142. Page
To ita-rayuwa-tana fusukantuwa ne zuwa rukunin imani da mala’iku, kuma tana tabbatar da shi a matsayin alama; domin tun da cewa rayuwa ita ce mafi muhimmancin sakamako a cikin halitta, kuma cewa ma’abota rayuwa su ne suka fi yaɗuwa, kuma mafiya yawaita kwafi-kwafi nasu saboda muhimmancinsu, kuma su ne suke raya gidan saukar baƙin na doron ƙasa da karaukai masu zuwa kuma masu ƙaura, kuma tun da ƙwallon doron ƙasa ya cika da nau’o’in ma’abota rayuwa irin haka, kumaana cika shi kuma ana yashe shi ko yaushe da kowane lokaci saboda hikimar sabunta da yawaita dangin ma’abota rayuwa, kuma ƙasa ta zama matadar da dukkan samammu ƙanana ta hanyar halittar ma’abota rayuwa da yawa, har cikin mafi ƙasƙancin abubuwan samar da su kuma mafi ruɓewarsu, kuma tun da cewa ana halittar ji a jiki da hankali waɗanda su ne mafi tsarkakar zallan matatar rayuwa da yawan gaske a doronwannan ƙwallon na ƙasa, kuma ana halittar rai wanda shi ne jauhari mafi taushi da tabbata nata, kamar dai ƙwallon doron ƙasa ana busa rayuwa a cikinsa kuma ya rayu ya ƙayatu da rayuwa da hankali da ji a jiki da kuma rayuka, don haka ba shakka cewa abu ne da ba ya cikin abu mai yiwuwa jikkunan sama waɗanda su ne mafi taushi da haske da girma a kan ƙasa, kuma mafi muhimmanci, a ce sun kasance matattu sandararru ba tare da rayuwa ko ji a jiki ba.
143. Page
Kenan ba makawa cewa akwai wasu mazauna ma’abota ji a jiki, kuma ma’abota rayuwa da suka dace da sammai, da suke rayuwa a cikinsu da sirrin rayuwa, kuma suke raya sammai da ranaku da taurari,kuma suna yaɗa rayuwa a cikinsu, kuma suna bayyana sakamakon halittar sammai, kuma suna samun jawabai na tsarkakuwa, waɗannan su ne mala’iku.
Sannan haƙiƙa sirrin haƙiƙanin rayuwa yana fuskantuwa zuwa rukunin imani da annabawa da manzanni, kuma yana tabbatar da shi a alamce.
Na’am; tun da cewa halitta an halicce ta ne saboda rayuwa, kuma ita rayuwa ita ce mafi girman tajalli kuma mafi ƙayatarwar zane, kuma mafi kyawun ƙirƙira ta rayayye mai tsayuwa da zatinSa na tun fil azal, kuma tun da cewa rayuwa ta har abada tana bayyana kanta ta hanyar aiko manzanni da saukar da littattafai, to da babu waɗancan littattafai kuma babu waɗancan manzanni da ba a san waccan rayuwa ta fil azal ba,kuma kamar yadda cewa rayuwar ɗan’adam ana fahimtar ta ne ta hanyar zancensa, hakanan haƙiƙa wanda yake bayyana kalmomi da saƙwannin wanda yake magana yake umarni kuma yake hani kuma yake jawabi ta bayan duniyar gaibi wanda yake ƙarƙashin labulen wannan halitta su ne annabawa da littattafai saukakku a hannayensu; don haka babu shakka cewa rayuwa a cikin wannan halitta kamar yadda take shaidawa shaidawa mai yanke shakku bisa wajabcin samuwar rayayye na tun fil azal, haƙiƙa ita kuma tana fuskantuwa zuwa rukunin “aiko manzanni da saukar da littattafai” wanda shi ne haskake-haskake na rayuwa ta tun fil azal,da tajallolinta da alaƙoƙinta da shi, kuma tana tabbatar da shi a alamce musamman ma manzancin Muhammadiyya da wahayin Alƙur’ani, ta yadda haƙiƙa su suna matsayin ruhi da hankali na rayuwa;,don haka za a iya cewa haƙiƙa cancantarsu tabbatacciya ce yanke kamar samuwar wannan rayuwa.
144. Page
Na’am; kamar yadda rayuwa ta ke ƙunari ne mai tsattsafowa daga halitta, kuma ji a zuci da jiki suke ƙunarin rayuwa da suke tsattsafowa daga gare ta, hankali kuwa shi ne ƙunarin ji a zuci da yake tsattsafowa daga gare shi,kamar yadda yake tsattsafowa daga ji a jiki, shi kuwa ruhi jawhari ne tatacce na rayuwa, kuma shi ne zatinta matabbaci mai cin gashin kansa; hakanan haƙiƙa rayuwar Muhammadiyya ta zahiri da ta ma’ana ita ce ƙunarin ƙunari mai tsattsafowa daga rayuwar halitta da ruhinta, kuma manzancin Muhammadiyya shi ne mafi tatuwar ƙunari mai tsattsafowa daga jin halitta na zuciya da na jiki da kuma hankalinta, kai rayuwa ma kacokan ita ce rayuwar halitta da shaidar guraban rayuwar Muhammadiyya ta zahiri da ta ma’ana, kuma manzancin Muhammadiyya ji ne a jiki ga jin halitta a jiki kuma shi ne haskenta,kuma wahayin Alƙur’ani ruhi ne na rayuwar halitta kuma hankali ne na jin halitta a jiki da shaidawar haƙiƙoƙinsa ma’abota rai,na’am,na’am,na’am.
145. Page
Da dai hasken manzancin Muhammadiyya zai fita dagahalitta ya rabu da ita da halitta ta mutu,kuma da Alƙur’ani zai tafi ya bar halitta to da halitta ta haukace, kuma da kan ƙwallon ƙasa ya rasa hankalinsa, kai da ma kansa wanda zai wanzu babu ji a zuciyarsa ya yi karo da ɗaya daga cikin taurari, da kuma Alƙiyama ta tashi.
Sannan kuma dai rayuwa tana fuskantuwa zuwa rukunin imani da ƙaddara,kuma tana tabbatar da shi a alamce; domin tun da cewa rayuwa haske ce ga duniyar zahiri,kuma mai mamaye ta ne kuma magamiya ce gare ta,kuma ita ce sakamakon samuwa kuma ita ce manufarta,kuma mafi tattarewar maduban tajallolin mahaliccin wannan halitta,kuma mafi ƙayatarwa kuma mafi tsantsaruwar samfuri da fihrisar sha’anoni da tsare-tsaren aiwatarwa na ubangijintaka,kuma ita -ba tare da ja in ja cikin kamantawa da kwatantawa ba-ta na matsayin shiri da tsarawa ne gare ta ta wata fuskar.
146. Page
yadda ƙwallo na asali na bishiya da jijiyoyinta, da ƙwallayenta da ‘ya’yanta suna samun wani nau’i na rayuwa kamar dai ita bishiyar kanta, kai suna ma ɗauke da wasu dokoki na rayuwa mafiya tsantsancewa daga dokokin rayuwa na bishiyar kanta, kuma kamar yadda ƙwallaye da jijiyoyi waɗanda lokacin damina da ya wuce ya bar su kafin lokacin kaka na yanzu, waɗanda kuma zai barsu da yawa ga lokutan kaka bayan wannan lokacin kakan, da suke ɗauke da tajallin rayuwa kamar dai wannan lokacin kakar, kuma suna miƙa wuya su bi dokokin rayuwa, to hakanan dukkan wani reshe na bishiyar halitta, yana da lokacin da ya wuce da lokaci mai zuwa, kuma yana da sarƙa da ta samu daga zango-zangonsa da yanaye-yanayensa da suka wuce da masu zuwa, kuma samuwa mai yawaita ta kowane nau’i da kowane yanki yana matsayin sarƙa ce ta samuwa a ilimance tare da yanaye-yanayensa mabambanta cikin ilimin Allah, ita kuwa samuwa a ilimance kamar samuwa a haƙiƙatana samun bayyana ta ma’ana ta rayuwa ta gaba ɗaya,ta yadda abubuwa masu ƙima na rayuwa ana cirosu ne daga waɗancan allunan, wato allunan ƙaddara ma’abotan rayuwa da ma’ana.
147. Page
Na’am; haƙiƙa cikar duniyar rayuka wadda ita nau’i ne na duniyar gaibi, cikarta da rayukan da su ne ainihin rayuwa kuma abubuwan da ake samar da ita da su da ainihinta da zatinta;babu shakka cewa shi yana buƙatar kuma yana lazimta rayuwa ta bayyana a cikin wani nau’in da kashi na biyu na duniyar gaibi wadda ake kira da zamanin da ya wuce da mai zuwa, kuma haƙiƙa tsari mafi ƙayatuwa cikin samuwa a ilimance ta kowa ne abu da yanaye-yanayensa masu ma’ana, da sakamakonsa da zango-zango nasa ma’abota rayuwa suna nuni bisa cewa rayuwa ta ma’ana tana tajalli a kan wannan abu ta wata fuska.
Na’am; haƙiƙa tajallolin rayuwa irin wannan waɗanda su ne hasken ranar rayuwa ta fil azal, babu kokwanto cewa su ba su taƙaita ba cikin duniyar bayyana da zamanin da ake ciki, da wannan samuwa ta zahiri, kuma ba sa iyakantuwa a kansu, maimakon haka kowace duniya tana samun tajalli daga tajallolin wancan haske daidai da shirinta; ita kuwa halitta da dukkan duniyoyinta ba ta kasancewa ma’abociyar rayuwa da haske sai da wancan tajallin, in ba haka ba kuwa da sai kowace duniya ta zamo kamar yadda kallon ɓata yake ganinta wata jana’iza ce babba mai firgitarwa da razanarwa, kuma wata duniya ce mai duhu abar ruguzawa ƙarƙashin wata rayuwa ta ɗan lokaci ta zahiri.
148. Page
Ta haka ne da sirrin rayuwa ake fahimtar wata fuska mai faɗi daga fuskokin rukunin imani da ƙaddara da zartarwa kuma ake tabbatar da shi, ma’ana kamar yadda rayuwantuwa na duniyar bayyane da samammun abubuwa mahalarta suke bayyana da tsaruwarsu da sakamakonsu, to hakanan ababan halittar zamanin da ya wuce da zamani mai zuwa wanda shi ma ana ɗaukarsa daga cikin duniyar gaibu suna da samuwa ta ma’ana ma’abociyar rayuwa ta ma’ana, da tabbata a ilimance ma’abociyar ruhi, ta yadda tasiri da gurbin wannan rayuwa ta ma’ana yake bayyana kuma yake tajalli da sunan abubuwan ƙaddarawa ta hanyar allon zartarwa da ƙaddarawa.
JUZU’I NA UKU DAGA RATAYE
Tambaya game da mas’alar tashin Alƙiyama
Haƙiƙa bayanan Alƙur’ani inda ya ceإِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ[1]: da kuma[2]وَمَآ أَمۡرُ ٱلسَّاعَةِ إِلَّا كَلَمۡحِ ٱلۡبَصَرِ
waɗanda suke maimaituwa suna bayyana cewa tashin alƙiyama babba zai faru ne cikin ‘yar ƙiftawa ta bazata, sai dai hankali ƙuntatacce yana son misali ne da ake gani don ya miƙa wuya ga wannan mas’ala mai ban mamaki mai shallake hankali mai ƙayatarwa mai gajiyarwa wadda ba ta da tamka kuma ya karɓe ta?
[1]{Ita ba ta kasance ba face tsawa guda ɗaya}[Y.S:29]
[2]{Lamarin tashin alƙiyama bai kasance ba face kamar ƙiftawar ido}[An-Nahlu:77]


