JUZU’I NA HUƊU NA RATAYE
NAVIGATION
153. Page
Ita kuwa mas’ala ta huɗu:wadda ita ce mutuwar duniya da tsayawar tashin Alƙiyama, to misalinta shi ne:
Cewa zai yiwu wani tauraroko tauraro mai wutsiya ya rusa mazaunarmu cikin ɗan taƙi idan ya yi karo da ƙwallon duniyarmu da gidan saukar baƙinmu da wani umarni na ubangiji; kamar rusa wata fada da aka gina cikin shekaru goma cikin daƙiƙa ɗaya.
JUZU’I NA HUƊU NA RATAYE
قَالَ مَن يُحۡيِ ٱلۡعِظَٰمَ وَهِيَ رَمِيمٞ * قُلۡ يُحۡيِيهَا ٱلَّذِيٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلۡقٍ عَلِيم
[1]ٌ
To kamar yadda ya zo a misali na uku na haƙiƙa ta tara daga kalma ta goma, da dai wani mutum zai haɗa wata runduna sabuwa mai girma a rana ɗaya, kuma idan wani ya ce maka:haƙiƙa wannan mutum da sautin wani kakaki zai tattara taron ɗaiɗaikun wannan rundunar da suka watsu domin hutawa, sai wannan taron rundunar ya shiga ƙarƙashin tsarinsa, to idan ka ce: ba zan gasgata ba; to haƙiƙa kai za ka fahimci cewa ka yi tasarrufi ne cikin wauta; hakanan haƙiƙa mai iko masani wanda ta hanyar umarnin كُن فَيَكُونُ-Kasance sai ya kasance-ya adana kuma ya shigar da ɓoyayyun abubuwa da ƙwayoyin zarra cikin jikkuna da suka yi kama da rundunoni na dukkan dabbobi da wasu rayayyun masu kama da runduna, kuma cikin kowane ƙarni, koma a ce cikin kowane lokacin kaka ya samar da gungu-gungu na ma’abota rayuwa da nau’i-nau’insu a doron ƙasa, waɗanda suka yi kama da dubban rundunoni, shin zai yiwu a ce game da wancan mai ikon masani ta yaya da ƙahon Israfilu zai tattara ƙwayoyin zarra na tushe da sassa na asali waɗanda suka san juna ta hanyar tsaruwarsu ƙarƙashin tsarin jiki da ya yi kama da wata runduna, kuma shin zai yiwu a nesanta faruwar haka daga gare shi; to idan dai an faɗi haka to haƙiƙa hakan hauka ne cikin wauta.
[1]{Ya ce: “Wane ne ke raya ƙasusuwa alhali kuwa suna rududdugaggu?”. Ka ce, “wanda ya ƙagi halittarsu a farkon lokaci, Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai ilimi ne.}[Y.S:78-79].
154. Page
Alƙur’ani mai girma wani lokacin yana ambatar ababan mamaki na ayyukan Allah masu gudana a duniya a matsayin shimfiɗa saboda ya sanya zuciya ta karɓi ayyukansa masu shallake hankali waɗanda za su faru a Lahira, kuma kamar a matsayin tanadi domin a saita ƙwaƙwalwa domin gasgatawa, kuma ya ambaci ayyuka masu ban mamaki na ubangiji na nan gaba da na Lahira ta hanyar da za mu gamsu da makamantansu masu yawa waɗanda su suna daga cikin abubuwan da muke gani.
Ga misali:أَوَ لَمۡ يَرَ ٱلۡإِنسَٰنُ أَنَّا خَلَقۡنَٰهُ مِن نُّطۡفَةٖ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٞ مُّبِين[1]zuwa ƙarshen surar, Alƙur’ani mai hikima yana tabbatar da tashin Alƙiyama a wannan gaɓar cikin
[1]{Ashe, kuma mutum bai ga (cewa) lalle Mu, Mun halicce shi daga maniyyi ba, sai ga shi mai yawan husuma, mai bayyanata}[Y.S:77]
155. Page
mas’alar tashin alƙiyama da misalai bakwai ko takwas da kuma tsaruka mabambanta; ta yadda yake bijiro da halitta ta farko a gaban idanunuwa da farko kuma yana cewa:Haƙiƙa ku kuna ganin halittarku daga maniyi zuwa gudan jini sannan zuwa gudan tsoka, kuma daga gudan tsoka zuwa halittar mutum, to ta yaya za ku yi musun wata halittar ta biyu?ita kwatankwacinta ce, koma a ce mafi sauƙi daga gare ta!
Sannan bayan ya yi nuni zuwa kyautaye-kyautaye masu girma waɗanda sarki na gaskiya mai girma da ɗaukaka ya kyautata su ga mutum da kalmar[1]ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلشَّجَرِ ٱلۡأَخۡضَرِ نَارٗا yana cewa:Wannan da ya yi ni’ima a gare ku da irin waɗannan ni’imomi ba zai barku sasakai ba har ku shiga ƙabari ku yi barci ba tare da kun tashi ba.
Sannan yana faɗa a alamce:haƙiƙa ku kuna ganin raya bishiyoyi matattu da mai da su kwarra, to ta ya yaba za ku iya ƙiyasin ƙasusuwa da suka yi kama da itatuwa ba da su, kuma kuke nisanta rayar da su?!
Kuma shin zai gajiyar da wanda ya halicci sammai da ƙasa ya rayar kuma ya matar da ɗan’adam wanda shi ne ɗan itaciya na sammai da ƙasa?!
[1]{Wanda ya sanya muku wuta daga ita ce kore}[Y.S:80]
156. Page
Don haka wanda yake damuwa da kulawa da bishiya gundumemiya shin zai yi watsi da ‘ya’yan itaciyarta ya bar su ga wasu?! kuma shin ku kuna tsammani cewa zai sanyaشجرة الخلقة-bishiyar halitta- ta zama abin wasa kuma mai gararamba, wannan da aka cakuɗa dukkan sassanta da hikima, ta hanyar barinsa dukkan sakamako na waccan bishiyar?!
Don haka haƙiƙa wanda zai rayaku a cikin tashin Alƙiyama shi ne wanda dukkan samammu suke miƙa wuya gare shi a matsayin rundunoni masu biyayya, kuma suke sunkuyar da kawunansu gaba ga umarninكُن فَيَكُونُkasance sai ya kasance, da cikakken miƙa wuya, kuma hallittar lokacin kaka shi ne mafi sauƙi a gare shi kamar dai halittar fure, da halittar dukkan dabbobi mai sauƙi ne bisa ikonsa kamar halittar ƙuda ɗaya, kuma kada mu ƙalubalanci ikon wanda ya siffanta da waɗannan siffofi muna masu cewa: مَن يُحۡيِ ٱلۡعِظَٰمَ wane ne yake raya ƙasusuwa alhali su suna rududdugaggu, domin gajiyarwa.
Sannan shi yana cewa da bayanin:فَسُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٖ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ[1] haƙiƙa Shi mai girma da ɗaukaka ma’abocin jalala wanda ragamar kowane abu ta ke
[1]{Tsarki ya tabbata ga wanda mulkin kowane abu yake hannunsa kuma zuwa gare shi ake mai da ku}
157. Page
hannunsa, kuma mabuɗan kowane abu suke hannunSa, yana jujjuya dare da rana da ɗari da zafi cikin sauƙi irin sauƙin juya shafuffukan littafi, kuma duniya da Lahira a gaban ƙudurarSa kamar gidaje biyu ne da za a kulle wannan a buɗe wancan.
Kuma tun da lamura haka suke to a matsayin sakamakon dukkan hujjojin shi neوَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُون[1] ma’ana haƙiƙa Shi zai rayar ku bayan ƙabari, kuma ya zo da ku zuwa tashin alƙiyama, kuma da sannu zai yi muku hisabi a halararSa mai girma.
Lallai haƙiƙa waɗannan ayoyi sun kintsa ƙwaƙwale domin yarda da tashin Alƙiyama, kuma sun saita zukata, domin sun bayyana kininsa a cikin ayyuka na duniya.
Sannan haƙiƙa Alƙur’ani mai girma a wasu lokutan yana ambatar ayyukan Allah na Lahira masu ban mamaki ta hanyar da take ilhamar kininsu na duniya domin kada ma wata makurɗa ta nesantawa da inkari ta yi saura.
Ga misali:[2]إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَت da إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَت
[3] da إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتۡ
[4],
domin a cikin waɗannan surori yana ambaton juye-juye manya-manya da tasarrufofin ubangijintaka waɗanda za su faru a Alƙiyama da tashi ta hanyar da mutum cikin sauƙi zai karɓi waɗancan juye-juye da suke firgita zuciya kuma hankali ba zai iya kamo bakin zaransu ba, wannan kuwa saboda shi yana ganin kwatankwacinsu a duniya misali cikin lokacin damina da lokacin kaka.
[1]kuma gare Shi a ke komar da ku”
[2]Idan rana aka shafe haskenta}[Attakwair:1]
[3]{Idan sama ta tsage}[Al-infiɗar:1].
[4]{Idan sama ta kece}[Al-Inshiƙaƙi:1
158. Page
Zancen yana da tsawo cikin wannan batu, koma nuni zuwa dunƙulallun ma’anoni na waɗancan surori nuni sassauƙa zai yi tsawo; don haka kawai zan ambaci kalma ɗaya ne a matsayin samfuri, ga misali: kalmarوَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَت[1] don aba da ma’anar cewa za a watsa dukkan ayyukan kowa da kowa a tashin Alƙiyama suna ababan rubutawa a kan takarda; kuma wannan mas’ala domin kasancewarta mai ban mamaki ƙwarai a kan kanta, to hankali shi kaɗai ba ya iya kai wa gare ta, sai dai kwatankwacin watsa takardu bayyananne ne ƙwarai cikin tashin lokacin kaka, kamar yadda wasu kinin kan bayyana tare da su, na wasu nuƙuɗoɗin kamar yadda surar ta ke nuni zuwa haka; domin kowace bishiya mai yin ‘ya’ya, kuma kowa ce ciyawa mai yin fure suna da ayyukan da aka ɗora musu, da bautatuwa daidai da yadda suka yi tasbihi suna masu bayyana sunayan Allahntaka a kansu, don haka dukkan ayyukansu ana rubuta su ne tare da tarihin rayuwarsu cikin dukkan ƙwallayensu da ‘ya’yan irinsu, kuma suna bayyana a wani lokacin kakar kuma a
[1]{Idan takardun ayyuka aka watsa su (ga masu su)}[Attakwair:10]
159. Page
wata ƙasar, kuma su kamar yadda cikin sura mai fasaha ƙwarai suke tuna mana ayyukan kakanninsu da tuwasansu ta hanyar yaren kamanni da launi da sura da suke bayyana su, hakanan za a yaɗa takardun ayyukansu da rassansu da ganyayyakinsu da furanninsu da ‘ya’yan itacensu, don haka wanda yake aiwatar da waɗannan abubuwa cikin hikima da siffar kiyayewa da tsarawa da tarbiyyanta da tausasawa a gaban idanunmu da ganinmu,kuma shi ne mai cewaوَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَت kuma yayin da aka yaɗa takardu, to ka ƙiyasta ragowar nuƙuɗoɗin a kan haka, kuma ka yi istinbaɗi in dai har kana da ikon yin hakan.
Kuma domin taimakonka bari mu faɗi wannan: kamar yadda wannan zance, ma’ana إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَت yayin da rana aka tafi da haskenta yake nuni da lafazin التكوير Tafi da haske – ma’ana lulluɓewa da ninkewa da tarawa-zuwa wata kwatantawa mai ban ƙaye; hakanan yake nuni zuwa kininsa:
Na farko: Na’am; haƙiƙa sarki na gaskiya mai ɗaukaka lallai daga wajenSa ya buɗe sitircewar rashi da iska da samaniya, kuma daga cikin taskokin rahamarSa ya fitar da fitila kamar rana mai kama da wata jauhara da take haskake duniya, kuma ya bayyana wannan fitila a cikin duniya, kuma bayan an rufe duniya, za a ninke wannan jauharar cikin sitircewarSa kuma zai ɗauke ta.
160. Page
Na biyu: kamar yadda cewa rana ma’aikaciya ce abar umarta ce, abar sanya ta aiki ce da yaɗa jin daɗi na haske, da kuma lulluɓe haske da duhu bisa canjin junansu a kan doron ƙasa, kuma cewa sarkin gaskiya mai ɗaukaka yana sanya waccan ma’aikaciya cikin kowane maraice ta tattara kayayyakinta kuma ta ɓuya, kuma wani lokacin ta kasance cikin gwagwarmaya tare da sitircewa ta giza-gizai, kuma wata ya kasance labule ne a gaban fuskarta wasu lokutan, don haka ita tana karkaɗe hannayenta daga aikinta a hankali a hankali, kuma tana tattara kayanta da rajistar ayyukanta; hakanan haƙiƙa ita wannan abar umartar watarana za a cire ta daga waɗancan umarce-umarcen babu makawa; ko da kuwa babu wani dalili na cireta ɗin, domin masu yi mata ƙyashi guda biyu da suke kan fuskarta a yanzu kuma waɗanda ba su gushe ba suna karkata zuwa girma da kaɗan da kaɗan za su girma, kuma da sannu rana za ta nannaɗe haskenta da ta nannaɗa shi a kan doron ƙasa da wani umarni na ubangiji, za ta naɗe shi da wani umarnin na ubangiji, kuma sarki na gaskiya maɗaukaki ya nannaɗe wannan haske a kan rana kuma ya ce da ita: wani aiki bai saura ba gareki a kan doron ƙasa, to taho ki tafi jahannama kuma ki ƙona waɗanda suka bauta miki kuma suka wulaƙanta abin umarta abin horewa kamarki, suna masu tuhumarsa da ha’inci da rashin cika alƙawari, da haka ne rana za ta karanta dokarإِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتIdan aka tafi da hasken ranaa kan fuskarta.


