JUZU’I NA UKU DAGA RATAYE

148. Page

Ta haka ne da sirrin rayuwa ake fahimtar wata fuska mai faɗi daga fuskokin rukunin imani da ƙaddara da zartarwa kuma ake tabbatar da shi, ma’ana kamar yadda rayuwantuwa na duniyar bayyane da samammun abubuwa mahalarta suke bayyana da tsaruwarsu da sakamakonsu, to hakanan ababan halittar zamanin da ya wuce da zamani mai zuwa wanda shi ma ana ɗaukarsa daga cikin duniyar gaibu suna da samuwa ta ma’ana ma’abociyar rayuwa ta ma’ana, da tabbata a ilimance ma’abociyar ruhi, ta yadda tasiri da gurbin wannan rayuwa ta ma’ana yake bayyana kuma yake tajalli da sunan abubuwan ƙaddarawa ta hanyar allon zartarwa da ƙaddarawa.

 

 

JUZU’I NA UKU DAGA RATAYE

 

Tambaya game da mas’alar tashin Alƙiyama

 

Haƙiƙa bayanan Alƙur’ani inda ya ceإِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ[1]: da kuma[2]وَمَآ أَمۡرُ ٱلسَّاعَةِ إِلَّا كَلَمۡحِ ٱلۡبَصَرِ

waɗanda suke maimaituwa suna bayyana cewa tashin alƙiyama babba zai faru ne cikin ‘yar ƙiftawa ta bazata, sai dai hankali ƙuntatacce yana son misali ne da ake gani don ya miƙa wuya ga wannan mas’ala mai ban mamaki mai shallake hankali mai ƙayatarwa mai gajiyarwa wadda ba ta da tamka kuma ya karɓe ta?

 


[1]{Ita ba ta kasance ba face tsawa guda ɗaya}[Y.S:29]

[2]{Lamarin tashin alƙiyama bai kasance ba face kamar ƙiftawar ido}[An-Nahlu:77]




149. Page

Amsa: Haƙiƙa cikin lamarin tashin Alƙiyama akwai “mas’aloli guda uku”, waɗanda su ne:

-       Zuwan ruhi ga jikkuna,

-       Da raya jikkuna,

-       Da farar da jikkuna.

 

Mas’ala ta farko: misalin zuwan ruhi ga jikkuna, shi ne:

Haɗuwar ɗaɗaikun runduna mai girma mai tsari waɗanda suka warwatsu suka yaɗu a dukkan sassa don hutawa da zarar sun ji sauti maɗaukaki na kakaki.

 

Na’am; haƙiƙa ƙahon Israfilu Aminci ya tabbata a gare shi shi ne kakakinsa, kamar yadda yake bai gaza sha’ani daga kakakin runduna ba, haƙiƙa rayuka da suka ji jawabinأَلَسۡتُ بِرَبِّكُمۡۖshin ba Ni ne ubangijinku ba wanda ya zo musu daga ɓangaren fil azal, kuma waɗanda suka amsaقَالُواْ بَلَىsuka ce na’am hakane, a lokacin da suka kasance a ɓangaren abada kuma cikin duniyar ƙwayar zarra; babu shakka cewa haƙiƙa waɗannan rayuka su ne mafiya horuwa da tsaruwa da biyayya daga ɗaiɗaikun waccan runduna sau dubunnai, sannan haƙiƙa “Kalma ta talatin”ta tabbatar da dalilai masu yanke shakku cewa ba wai kawai rayuka su kaɗai ba ne runduna ta tsarkakar ubangiji,a a dukkanin ƙwayoyin zarra su ma hakanan runduna ne na tsarkaka ta ubangiji, kuma sojoji ne masu biyayya ga umarninsa.

 

Mas’ala ta biyu: Kuma misalin raya jikkuna kuwa shi ne:

Kamar yadda zai yiwu a raya ɗaruruwan dubban fitilu na lantarki da haskaka su daga cibiya ɗaya a cikin wani birni babba ƙwarai kuma a daren wani biki katsam kamar ka ce su ba cikin wani tsawon lokaci suke ba, to haka zai yiwu a haskaka ɗaruruwan miliyoyin fitilun da ke kan doron ƙasa dukkaninsu daga cibiya ɗaya.

 


150. Page

Kuma tun da cewa wata halitta daga ababan halittar sarki na gaskiya mai girma da ɗaukaka kuma hadimi gare shi kuma ma’aikacin kunna fitila a gidan saukar baƙinsa kamarالكهرباء lantarki yana siffantuwa da wannan siffar daga abin da ya koya daga mahaliccinsa na daga darasin tarbiyya da tsaruwa, don haka ba shakka cewa zai yiwu tashin Alƙiyama mafi girma ya faru cikin ƙiftawar ido cikin dokoki masu ƙayatarwa masu tattara hikimar ubangijintaka wadda dubban hadimansa na haske suke alamtasu kamar lantarki.

 

Mas’ala ta uku:kuma misalin samar da jikkuna a lokaci ɗaya kuwa ita ce:

151. Page

Samar da ganyayyakin dukkan bishiyoyi-waɗanda su ne mafi yawa daga dukkan bil Adama sau dubu-nan take, samarwa abar matuƙar kyautatawa cikin lokacin kaka kamar kaka da ta wuce cikin ‘yan kwanaki kaɗan -da ba su kai kwana goma ba-, da samar da dukkan furannina dukkan bishiyu da ‘ya’yan itatuwansu da ganyayyakinsu kamar albarkatun gona na lokacin kaka da ta wuce cikin saurin wulƙitawar walƙiya,da farkawar mara adadi na ƙananan irin shuka da ƙwallayen ‘ya’yan itaciya da jijiyoyin bishiya, waɗanda su ne mafarar wancan lokacin kakan , da yayewarsu da rayar da su take ba tsammani a lokaci guda, da tajallinالبعث بعد الموتtashin matattu bayan mutuwaa bisa jana’izozin dukkan bishiyun da suke su kamar gawawwakin matattu ne da suke tsaye, waɗanda su kamar ƙasusuwa ne, da umarni ɗaya a tashi ɗaya,kuma da yaɗasu tare da raya adadi mara iyaka na ɗaiɗaikun gungu-gungu na ƙananan dabbobi ƙwarai rayawa mai matuƙar ƙayatarwa, musamman ma tayar da ƙabilun ƙudaje, kuma musamman ma ɗaiɗaikun na ƙabilar ƙudaje da ke yaɗuwa cikin shekara ɗaya a gaban idanunmu, kuma waɗanda suke goge fuskokinsu suke tuna mana alwala da tsafta ta hanyar tsaftace fuskokinsu da idanunsu da fuka-fukansu,domin duk da cewa waɗannan ɗaiɗaiku sun fi dukkan ɗaiɗaikun bani Adama da suka zo tun lokacin annabi Adamu (S.A.W) zuwa lokacinmu na yanzu yawa, sai dai su samar da su da tayar da su yana kasancewa ne duk lokacin kaka ne tare da wasu ƙabilun nasu daban cikin ‘yan kwanaki da ba su kai goma ba, babu shakka cewa shi ba misali ɗaya ne ba kawai na samar da jikkunan ‘yan’dam ranar Alƙiyama, sai dai, a a shi dubban misalai ne.


152. Page

Na’am; haƙiƙa gidan duniya gidan hikima ne, ita kuwa Lahira gidan iko ne; don haka kasancewar samar da abubuwa da sannu sannu yake faruwa kuma da shuɗewar lokaci a cikin duniya zuwa wani mataki yana buƙatar sunaye da yawa kamar sunan mai hikima da mai jerawa da mai gudanarwa da mai tarbiyanta, ya zama daga abin da hikimar ubangiji take wajabtawa, a Lahira kuwa haƙiƙa abubuwa suna faruwa ne katsahan kuma cikin ɗan taƙi ba tare da buƙatar mahaɗi ko lokaci ko zamani ko saurare domin tajallin iko da rahama fiye yake da na hikima acan,domin Alƙur’ani mai gajiyarwar bayaninsa yana nuni da bayanin

وَمَآ أَمۡرُ ٱلسَّاعَةِ إِلا كَلَمۡحِ ٱلۡبَصَر

Kuma lamarin tashin Alƙiyama bai kasance ba face kamar walƙawar gani, ko kuwa shi ne mafi kusa!zuwa cewa al’amuran da ake kammala su cikin yini ɗaya da shekara ɗaya a duniya, ana samar da su a lokaci guda kuma cikin walƙawa guda a Lahira, don haka in kana so ka gane zuwan tashin Alƙiyama ganewa mai yanke shakku kamar zuwan lokacin kaka mai zuwa to ka zurfafa nazari cikin “Kalma ta goma”, da “Kalma ta ashirin da tara”, waɗanda suka keɓanci tashin Alƙiyama kuma ka yi tsokaci, to idan  ba ka  gasgata zuwan Tashin Alƙiyama ba kamar yadda kake gasgata zuwan lokacin kaka to zo ka shigar da yatsunka cikin idanuna.


153. Page

 

Ita kuwa mas’ala ta huɗu:wadda ita ce mutuwar duniya da tsayawar tashin Alƙiyama, to misalinta shi ne:

 

Cewa zai yiwu wani tauraroko tauraro mai wutsiya ya rusa mazaunarmu cikin ɗan taƙi idan ya yi karo da ƙwallon duniyarmu da gidan saukar baƙinmu da wani umarni na ubangiji; kamar rusa wata fada da aka gina cikin shekaru goma cikin daƙiƙa ɗaya.

 

JUZU’I NA HUƊU NA RATAYE

قَالَ مَن يُحۡيِ ٱلۡعِظَٰمَ وَهِيَ رَمِيمٞ * قُلۡ يُحۡيِيهَا ٱلَّذِيٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلۡقٍ عَلِيم

[1]ٌ

To kamar yadda ya zo a misali na uku na haƙiƙa ta tara daga kalma ta goma, da dai wani mutum zai haɗa wata runduna sabuwa mai girma a rana ɗaya, kuma idan wani ya ce maka:haƙiƙa wannan mutum da sautin wani kakaki zai tattara taron ɗaiɗaikun wannan rundunar da suka watsu domin hutawa, sai wannan taron rundunar ya shiga ƙarƙashin tsarinsa, to idan ka ce: ba zan gasgata ba; to haƙiƙa kai za ka fahimci cewa ka yi tasarrufi ne cikin wauta; hakanan haƙiƙa mai iko masani wanda ta hanyar umarnin كُن فَيَكُونُ-Kasance sai ya kasance-ya adana kuma ya shigar da ɓoyayyun abubuwa da ƙwayoyin zarra cikin jikkuna da suka yi kama da rundunoni na dukkan dabbobi da wasu rayayyun masu kama da runduna, kuma cikin kowane ƙarni, koma a ce cikin kowane lokacin kaka ya samar da gungu-gungu na ma’abota rayuwa da nau’i-nau’insu a doron ƙasa, waɗanda suka yi kama da dubban rundunoni, shin zai yiwu a ce game da wancan mai ikon masani ta yaya da ƙahon Israfilu zai tattara ƙwayoyin zarra na tushe da sassa na asali waɗanda suka san juna ta hanyar tsaruwarsu ƙarƙashin tsarin jiki da ya yi kama da wata runduna, kuma shin zai yiwu a nesanta faruwar haka daga gare shi; to idan dai an faɗi haka to haƙiƙa hakan hauka ne cikin wauta.

 


[1]{Ya ce: “Wane ne ke raya ƙasusuwa alhali kuwa suna rududdugaggu?”. Ka ce, “wanda ya ƙagi halittarsu a farkon lokaci, Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai ilimi ne.}[Y.S:78-79].