Kalma ta Goma
NAVIGATION
2. Page
Kalma ta Goma
mabincika a kan tashin alƙiyama
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙai
فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتإِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلّشَيۡءقَدِير[1]
Ya kai ɗan’uwa, idan kana neman bayani game da tashin alƙiyama dalahira bayani sassauƙa cikin harshan da gama garin mutane za su fahimtakuma cikin salona filla-filla, to zo mu yi tsinkaye tare cikin wannan hikaya mai kwaikwayawa, kuma ka yi sauraro:
Wata rana wasu mutane biyu suka tafi zuwa wata masarauta[2] mai kama da aljanna, sai suka samu cewa duk mutane sun bar ƙofofin gidajensu da kantunansu da wuraran sana'o'insu a buɗe, ba su damu da kare su da ba su tsaro ba, ga dukiyoyinsu da kuɗaɗensu han-hai babu masu su, ko ma masu ba su kariya,sai ɗaya daga cikin mutanan nan biyu ya miƙa hannayensa zuwa ga duk abin da ransa ya biya masa, ya sata ya sana, ya aikata duk wani nau'i na zalunci da wauta yana mai biyewa son zuciyarsa, su kuwa mutanan garin ba su kula shi ba, sai abokin nasa ya ce masa:
Mai kake aikatawa ne haka?! Za fa ka gamu da uƙuba, kuma ka janyo min jangwam, domin wannan dukiyoyi na ƙasa ne, waɗannan mutan gari kuma sun zama runduna ce ko ma'aikata gaba ɗayansu da 'ya'yayansu an ɗauke su ne aiki cikin waɗannan lamura kamar fararen hula, don haka ne ma ba su damu da kai ba sosai kuma ba su
[1]"To ka yi duba zuwa ga guraban rahamar Allah yadda yake rayar da ƙasa bayan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki),tabbas Mai rayar da matattu ne,kuma Shi Mai iko ne a kan kome".
1masarauta a nan na nuni zuwa ga duniya (mawallafi).
3. Page
cutar da kai ba, sai dai faka san da sanin cewa tsari a wannan ƙasa tsattsaura ne, domin sarkin yana da 'yan sa ido da ma'aikata a ko ina, don haka ka yi gaggawar zuwa gare shi ka nemi afuwa, sai dai wawan ya kafe, kuma ya ce:
"A'a waɗannan dukiyoyi ba na ƙasa ba ne,su mallakin waƙafi ne babu mai su ko mammallakinsu,kowa zai iya yin abin da ya so da su,kuma ban ga abin da zai hana ni amfana daga waɗannan kyawawan abubuwa ba, ni ba zan gasgata abin da kake faɗa ba in ban gan shi da idona ƙuru-ƙuru ba",ya dai ci gaba da wannan soki burutsu kai ka ce wani bafalsafe ne, sai muƙabala mai zafi ta fara tsakaninsu, sai wannan wawa ya ce:
Da farkon fari dai:
"wanene wannan mamallakin ne? Domin ni ban san shi ba kuma ban yarda da samuwarsa ba!."
Sai abokin nasa ya ba shi amsa da cewa:"Haƙiƙa kai dai ka sani cewa gari bai taɓa zama babu dagaci ba,hakanan allura ba ta taɓa samuwa ba tare da wanda ya yi ta ko mamallakinta ba,harafi ba ya samuwa ba tare da marubuci ba, to tayaya ko za a sami wannan masarauta mai kyawu haka matuƙa ba tare da mai mulkinta ba?!
4. Page
Kuma ta yaya za a sami wannan tarin dukiya mai yawan gaske haka-kamar ka ce wani jirgin ƙasa[1] ne da aka shaƙe da kaya yake zuwa da dukiya mai ƙayatarwa kowa ne lokaci daga inda ba a sani ba ya juye su ya tafi-ya ya za a ce haka ta faru ba tare da mamallaki kuma mai ita ba?!
Hakanan waɗannan sanarwoyi da allunan talla da ke kafe ko ina, da waɗannan hatumai da kawunana sarki da ake ganinsu a kan waɗannan dukiyoyi da hajoji, da tutoci masu karkaɗawa da hahharbawa a kowace kusurwa, yaya za a ce ba su da mamallaki?!
Da alamu ka koyi wani abu daga harshan Turanci da falsafar yammacin Turai,amma ba za ka iya karanta waɗannan harafai da rubutu na musulunci ba,kuma ba ka tambayar wanda ya koya kuma ya san su ba, to zo na karanta maka mafi ɗaukakar doka da bayani",sai wannan wawan ya mai da martini ya na mai cewa:
"To mu ɗauka ma cewa:akwai wannan sarki da kake faɗa, to mai zai cutar da shi don na amfana da abu ɗan kaɗan sassauƙa, mai hakan zai rage daga taskarsa?kuma na ga babu kurkuku ko tsarewa ko uƙuba a nan".
2wannan nuni ne zuwa ga shekara, domin lokacin kaka kamar wani jirgin ƙasa ne da yake zuwa daga inda ba a sani ba wanda yak e kamar taska ce ta cimaka (mawallafi).
5. Page
Sai wannan aboki nasa ya amsa masa da cewa:"Ya kai wannan aboki, haƙiƙa wannan masarauta da ake gani a ke tsinkaye,ba komai ba ce face fage na atisaye da ɗaukar horo, kuma gurin baje koli ne na ƙere-ƙere na wannan sarki, kuma gidan saukar baƙi ne na shi na wucin gadi, ba tabbatacce ba, shin ba ka gani cewa kullum wani ayari yana zuwa wani kuma ya tafi, kullum a na cika shi kuma a fita daga cikinsa, kuma zuwa wani lokaci za a sauya wannan masarauta da wata,waɗannan mazauna da 'yan ƙasa za a ɗebe su zuwa wata masarautar madauwamiya ta dindindin, kowa ya sami uƙubarsa ko kyakkyawan sakamakonsa a can daidai da abin da ya aikata a nan."
Sai wancan maha'incin ya sake ce masa cikin bijirewa:"bazan gasgata ba, shin yanzu za a iya rusa wannan masarauta, kuma ,mazaunanta su tafi zuwa wata masarautar?"
Sai amintaccen abokin nasa ya ce:"Tun da yake kai taurin kan naka da bijirewar taka ta kai haka, to zan bayyana maka hujjojin da ba za su ƙirgu ba "cikin misalai goma sha biyu" don in tabbatar maka da cewa akwai wata kotu babba da gidan sakamako kyakkyawan sakamako da kyautatawa, da kuma gidan uƙuba da kaso, kuma wata rana za ta zo da za a bar wannan masarauta -da muke ciki- ɗungurungum, a rusa ta kamar yadda wasu ke barinta a kowacce rana.


