KAMMALAWA
NAVIGATION
106. Page
KAMMALAWA
Haƙiƙa haƙiƙoƙi goma sha biyu da suka gabata sashinsu yana goyon bayan sashi ne,kuma sashinsu yana cikasa da ƙarfafa sashi, kuma dukkaninsu sun bayyana sakamako ta hanyar haɗewar sashinsu da sashi, to wane zato ne na riyawa zai iya keta waɗannan ganuwoyi goma sha biyu masu kauri da ƙarfi kamar ƙarfe, ko kamar daiman, kuma ya huda su har ya girgiza imani da tashin alƙiyama wanda shi Katanga ce mai katangewa, kuma fadace da ba a iya keta ta, domin aya mai girma tana cewa:مَّاخَلۡقُكُم وَلَا بَعۡثُكُمۡ إِلَّا كَنَفۡسٖ وَٰحِدَةٍۚ[1]
tana fa’idantar da cewa halittar dukkan ‘yan’dam da tashinsu mai sauƙi ne kuma mara wahala ne ga ƙudurar Allahntaka kamar sauƙin halittar mutum ɗaya da tashinsa.
Na’am; Haka ne,kuma haƙiƙa na yi rubutu a game da mabincikar tashin alƙiyama a cikin Risalar“Al-Nuƙɗah” dalla-dalla game da haƙiƙar da wannan aya ta yi bayani game da ita, sai dai mu a nan za mu yi nuni zuwa taƙaitacciyar ma’anar ta tare da misalai, in ka so ka koma zuwa waccan risalar ta “Al-Nuƙɗa”, ga misali:kuma misali mafi ɗaukaka na Allah ne,kuma babu ja-in-ja cikin misali, kamar yadda da tajallin rana da zaɓinta ne da nufinta, da ita kamar yadda ta ke tajalli game da ƙwayar zarra ɗaya cikin sauƙi, tana tajjalli haka ma a bisa abubuwa masu garai-garai waɗanda ba su da iyaka da irin wannan sauƙin da sirrin haskakuwa.
[1]القمان:28”Kuma halittarku da tashinku ba komai ba ne face kamar rai ɗaya”
107. Page
Kuma haƙiƙa ɗan ɓirɓishi na ƙwayar zarra mai garai-garai ya yi kankankan da kan birbishin kogi mai yalwa wajen karɓar haskowar rana da sirrin الشفافيةgarai-garai,kuma kamar yadda yaro zai iya jujjuya kuma ya motsa ‘yar tsana wadda take da siffar jirgin ruwa da ‘yan yatsunsa, hakanan zai iya jujjuya da motsa jirgin ruwa na yaƙi tafkeke da sirrin الإنتظامtsaruwa, kuma kamar yadda kwamanda zai iya motsa soja ɗaya da umarnin “ku yi gaba” ,to haka zai iya motsa runduna babba da kalma kanta, da sirrin الإمتثالkarɓar umarni, kuma mu ɗauka cewa akwai wani ma’auni na haƙiƙa mai tsananin takatsantsan kuma babba a sararin samaniya ta yadda zai iya tantance kwakwa biyu idan aka ɗora su a kan tafukansa guda biyu, kuma zai iya auna rana guda biyu kuma ya yalwace su da sirrin الموازنةkwatantawa,to da za a sami wani ƙarfi da zai ɗaga ɗaya daga cikin waɗannan kwakwar biyu da suke tafukan zuwa sama ɗayar kuma ya yi ƙasa da ita, kuma aka sami rana biyu tare, to haƙiƙa wannan ƙarfi zai iya ɗaga ɗaya daga waɗannan rana-rana guda biyu zuwa sama, kuma ya yi ƙasa da ɗayar zuwa ƙasa.
108. Page
Kuma tun da mafi ƙanƙantar abu yana daidaita da mafi girman abu a cikin waɗannan samammun abubuwa sababbu tauyayyu masu ƙarewa da sirrin النورانيةHaskaka, da الشفافيةGarai-garai, da الإنتظامTsaruwa, daالإمتثالKarɓar umarni, daالموازنةKwatantawa,, kuma abubuwa da ba za su ƙirgu ba kuma ba za su ƙididdugu ba suna daidaituwa da abu ɗaya, don haka ba kokwanto cewa kaɗan da mai yawa, da babba da ƙarami kamar yadda yake daidaita a wajen ikon mai iko wanda yake sake babu ƙaidi da sirrin tajalloli na haske na ƙudurar zatinSa, wadda ba ta da iyaka, kuma wadda ta ke cikin matuƙar kamala, da sirrin garai-garai na masarautancin abubuwa, da tsaruwar hikima da iko, da cikar kamantawar abubuwa ga umarninsa na halittawa, da daidaiton yiwuwar abubuwa wanda yake nufin daidaiton ababan halitta wajen samuwarsu da rashinsu, hakanan zai iya tashin dukkan mutane da tsawa ɗaya kamar tashin mutum ɗaya.
Sannan matakan abu, ta fuskar ƙarfinsa da rauninsa suna bayyana ne ta hanyar shishshigar da abubuwa masu kishiyantar junansu cikinsa, misali ma’aunan zafi suna bayyana ne da shishshigar sanyi cikinsu, matakan kyawu suna bayyana ne da shishshigar muni, kuma matakan haske suna bayyana ne da shishshigar duhu; sai dai idan abu ya zama na zati ne -ma’ana yana da jiki-, ba siffa ba ne to haƙiƙa kishiyarsa ba za ta iya shiga cikinsa ba; domin wannan zai janyo haɗuwar kishiyoyi biyu a guri ɗaya wanda wannan abu ne da ba zai yiwu ba, kenan ba a samun matakai a cikin abin da yake mai zati ne a asalinsa, kuma tun da ikon mai iko na sake babu ƙaidi abu ne ainihin zatinsa, ba na siffa ba ne mai bijirowa daga baya kamar sauran samammu, kuma abu ne da yake cikin kamala ta sake babu ƙaidi, kenan gajiyawa wadda ita kishiyar iko ce abu ne mara yiwuwa ta shiga zatinSa, don haka haƙiƙa halittar lokacin kaka abu ne mai sauƙi mara wuya ga Sarkin gaskiya ma’abocin jalala kamar sauƙin halittar fure ɗaya.
109. Page
Amma idan za a jingina – abubuwa – zuwa sababai, to halittar fure ɗaya zai zama mai wahala kamar halittar lokacin kaka, sannan kuma raya dukkan ‘yan’dam da tashinsu abu ne mai sauƙi kamar raya rai ɗaya.
Haƙiƙa bayananmu da fayyacewarmu game da surorin kwaikwayawa da haƙiƙoƙinsu tun farkon batun tashin Alƙiyama har zuwa yanzu sun kwaranyo ne daga Alƙur’ani mai hikima, waɗanda ma’anarsu ita ce kintsa rai domin ta miƙa wuya, da kintsa zuciya domin ta karɓa, magana ta haƙiƙa kuwa ita ce Alƙur’ani, kenan Alƙur’ani shi ne magana, kuma shi kaɗai yake da ta cewa, don haka mu ji shi kuma mu saurare shi; domin hujja mai isa matuƙa ta Allah ce:
فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡض بَعۡدَمَوۡتِهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِير
[1]{Sai ka yi duba zuwa alamomin rahamar Allah yadda Yake rayar da ƙasa bayan mutuwarta.Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas Mai rayar da halitta ne, kuma Shi Mai iko ne a kan kowane abu}[Ar Rum:50].
110. Page
[1] قَالَ مَن يُحۡيِ ٱلۡعِظَٰمَ وَهِيَ رَمِيمٞ * قُلۡ يُحۡيِيهَا ٱلَّذِيٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلۡقٍ عَلِيمٌ
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ * يَوۡمَ تَرَوۡنَهَا تَذۡهَلُ كُلُّ مُرۡضِعَةٍ عَمَّآ أَرۡضَعَتۡ وَتَضَعُكُلُّ ذَاتِ حَمۡلٍ حَمۡلَهَا وَتَرَى ٱلنَّاسَ سُكَٰرَىٰ وَمَا هُمبِسُكَٰرَىٰ وَلَٰكِنَّ عَذَابَ ٱللَّهِ شَدِيدٞ
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۗ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ حَدِيثٗا
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٖ [4]* وَإِنَّٱلۡفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٖ
إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا* وَأَخۡرَجَتٱلۡأَرۡضُ أَثۡقَالَهَا * وَقَالَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا لَهَا * يَوۡمَئِذٖ تُحَدِّثُ أَخۡبَارَهَا * بِأَنَّ رَبَّكَ أَوۡحَىٰ لَهَا* يَوۡمَئِذٖ يَصۡدُرُ ٱلنَّاسُ أَشۡتَاتٗا لِّيُرَوۡاْ أَعۡمَٰلَهُمۡ* فَمَن يَعۡمَل مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ * وَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ شَرّٗا يَرَهُۥ[5]
*مَا ٱلۡقَارِعَةُ * وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡقَارِعَةُ * يَوۡم يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلۡفَرَاشِ ٱلۡمَبۡثُوثِ * وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالَُُٱلۡقَارِعَة
كَٱلۡعِهۡنِ ٱلۡمَنفُوشِ * فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ * فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ * وَأَمَّا مَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ * فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٞ* وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا هِيَهۡ*نَارٌ حَامِيَةُۢ
[6]
وَلِلَّهِ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَآ أَمۡرُ ٱلسَّاعَةِ إِلَّا كَلَمۡحِٱلۡبَصَرِ أَوۡ هُوَ أَقۡرَبُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Lallai mu saurari ayoyin Alƙur’ani bayyanannu irin waɗannan, kuma mu ce mun yi imani mun gasgata.
آمنت بالله و ملائكته و كتبه و رسله و اليوم الآخر و بالقدر خيره و شره من الله تعالى ، والبعث بعد الموت حق ، و أن الجنة حق ، و النار حق ، أن الشفاعة حق ، أن منكرا و نكيرا حق، أن الله يبعث من في القبور ، أشهد أن لا إله إلا الله و أشهد أن محمد رسول الله
اللهم صل على ألطف و أشرف و أكمل ثمرات طوبى رحمتك الذي أرسلته رحمة للعالمين و وسيلة لوصولنا إلي أزين و أحسن و أجلى و أعلى ثمرات تلك الطوبى المتدلية على دار الآخرة أي الجنة.
[1]{Ya ce “Wane ne yake rayar da ƙasusuwa alhali suna rududdugaggu?”K ace, “Wanda ya ƙaga halittarsu a farkon lokaci, Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai sani ne.}[Yasin:78-79].
[2]{Yak u mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku.Lalle girgizar Ƙasa ta tsayuwar Al-Ƙiyama wata aba ce mai girma.A ranar da kuke ganin ta dukkan mai shayar da mama tana shagala ga barin abin da ta shayar, kuma dukkan mai ciki tana haihuwar cikinta, kuma kana ganin mutane suna masu maye alhali kuwa su ba masu maye ba ne, amma azabar Allah ce mai tsanani}[Al-Hajj:1-2]
[3]سورة النساء :88
[4]{Lalle ne masu ɗa’a ga Allah, dahir, suna cikin ni’ima.Kuma lalle ne fajirai, dahir, suna cikin Jahim}[Al-Infiɗar:13-14].
[5]{Idan aka girgiza ƙasa, girgizawa.Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.Kuma mutum ya ce “Mene ne ya same ta? A ranar nan, za ta faɗi labarinta.Cewa Ubangijinka ya yi umarni zuwa gare ta.A ranar nan, mutane za su fito daban-daban domin a nuna musu ayyukansu.To wandaya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.Kuma wanda ya aikatagwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi} [Az Zalzalah:1-8].
[6]{Mai ƙwanƙwasawar (zukata da tsoro)!Me ne ne mai ƙwanƙwasawa?Kuma me ya sanar da kai abin da ake cewa mai ƙwanƙwasawa?Ranar da mutane za su kasance kamar ‘yayan fari masu watsuwa.Kuma duwatsu su kasance kamar gashin sufin da aka saɓe.To amma wanda ma’aunansa suka yi nauyi.To, shi yana cikin wata rayuwa yardadda.Kuma wanda ma’aunansa suka yi sauƙi(babu nauyi).To uwarsa Hawiya ce.Kuma me ya sanar da kai me ne ne ita?Wata wuta ce mai zafi.}[Al-Ƙariah:1-11].
[7]{Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al’amarin Sa’a bai zama ba face kamar ƙiftawar gani, ko kuwa shi ne mafi kusa.Lalle Allah a kan dukkan komai, Mai iko ne.}[An-Nahl:77].
111. Page
اللهم أجرنا و أجر ولدينا من النار و أدخلنا و أدخل والدينا الجنة مع الأبرار بجاه نبيك المختار ، آمين[1]
Ya kai ɗan’uwa wanda ya karanta wannan saƙo da adalci da zurfafa nazari, ka da ka ce ban fahimci wannan “Kalma ta goma” ba fahimta cikakkiya,ka da ka ƙuntata ko ka ƙosa saboda haka; domin mai kaifin basira kuma bafalsafe kamar Ibnu Sina ya taɓa cewa: “Tashin Al-Ƙiyama ba zai kasance ba ne a kan ma’aunan hankali, kuma hankali ba zai iya shiga wannan fagen ba”,Hakanan dukkan malaman Musulunci sun hukunta -bisa haɗuwar maganarsu-cewa tashin Al-Ƙiyama mas’ala ce ta ruwaya, kuma dalilanta ma dalilai ne na ruwaya, kuma ba za a iya kaiwa gare ta ba da hankali, duk da dai waɗannan abubuwa haƙiƙa wata hanya zuzzurfa kuma maɗaukakiya ƙwarai-ta fuskar ma’ana-ba zai yiwu ta zama-bagatatan-a matsayin tafarki na hankali ga kowa da kowa ba, kuma ya wajaba mu godewa mahalicci mai jin ƙai godiya dubu bisa kyautatawarSa da baiwarSa saboda ya ba mu damar tafiya cikin wannan tafarkin zuzzurfa maɗaukaki cikin wannan sauƙi da rahamarSa, kuma Alƙur’ani mai hikima yana kwaranya a wannan zamanin wanda kwaikwayo ya karye a cikinsa kuma miƙa wuya ya ɓaci;domin ya ishe mu wajen tserar da imaninmu, kuma ya wajaba mu yarda da abin da muka fahimta, kuma mu yi aiki wajen ƙara shi ta hanyar sake karatu da maimaita bita.
Haƙiƙa ɗaya daga sirrinkan rashin tafiya da hankali cikin batun tashin Alƙiyama,shi ne cewa shi tashin Alƙiyama mafi girma yana daga tajallin suna mafi girma, don haka haƙiƙa tashin Alƙiyama babba ta hanyar gani da kuma nuna ayyuka manya mabayyana ta hanyar tajallin sunan Allah mafi girma, datajallin daraja mafi girma ga kowanne suna da yake tabbatarwa tabbatarwa mai sauƙi kuma miƙa wuya gare shi ya zama yankakke kuma imani da shi ya zama tabbatacce ne kamar dai lokacin kaka.Ta haka ne, a ke ganinsa kuma a bayyana shi ta hanyar kwaranyar Alƙur’ani a cikin wannan “Kalma ta goma”, to da dai hankali zai ci gashin kansa ya kaɗaita da tsare-tsarensa ƙuntatattu sauƙaƙa da ya dawwama mai gazawa kuma da ya buƙatu zuwa kwaikwayo.
[1]Na ba da gaskiya da Allah da mala’ikunSa da littattafanSa da ranar lahira da ƙaddara mai daɗinta da mara daɗinta cewa daga Allah maɗaukakin sarki ta ke, kuma tashin matattu bayan mutuwa gaskiya ne, kuma aljanna gaskiya ce, kuma wuta gaskiya ce, kuma ceto gaskiya ne, kuma Munkaru da Nakiru gaskiya ne, kuma Allah zai tashi waɗanda suke cikin ƙaburbura, na shaida babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, kuma na shaida cewa Muhammadu manzon Allah ne.
Ya Allah ka yi tsira a bisa mafi tausasawar kuma mafi darajar kuma mafi kamalar ‘ya’yan bishiyar Ɗuba, wanda Ka aiko shi a matsayin rahama ga talikai, tsanin isuwarmu zuwa mafi ado kuma mafi kyawu kuma mafi bayyana kuma mafi ɗaukakar ‘ya’yan bishiyar waccan Ɗubar mai sassaukowa a bisa gidan ƙarshe wato aljanna.
Ya Allah ka tsare mu ka tsare iyayenmu daga wuta, kuma ka shigar da mu da iyayenmu aljanna tare da mutanen kirki, da alfarmar annabinKa abin zaɓi, amin.
112. Page
RATAYE MUHIMMI DAGA “KALMA TA GOMA” DA JUZU’I NA FARKO DAGA RATAYENTA


