MISALI NA BAKWAI
NAVIGATION
14. Page
MISALI NA BAKWAI
Zo mu ɗan yawata kaɗan, mu ga abin da ke faruwa tsakanin waɗannan mazauna farar hula.
Kalli, an sanya kyamarori a ko ina da kowace kusurwa suna ta ɗaukar hoto, kalli, ko ina akwai marubuta masu ɗinbin yawa suna rubuta wasu abubuwa, suna aje bayanai,
15. Page
suna tantance kowanne abu har mafi ƙanƙantar ayyuka da mafi sauƙin abubuwa masu faruwa.
Kalli,an kafa wata kyamara babba[1] a kan wancan babban dutse, wadda ta ke ta musamman ce wajen wannan sarki, tana ɗaukar dukkan abin da yake gudana a dukkan waɗannan gurare, ashe kenan shi ya yi umarni da a rubuta a tantance dukkan mu'amaloli da lamura da suke gudana a masarautarsa, wannan kuwa na nufin cewa wannan sarki mai girma ya yi umarni da a rubuta dukkan abubuwan da suke faruwa kuma a ɗau hotunansu, to lallai ba makawa wannan kiyaye bayanai cikin matuƙar tantancewa ana yin sa ne don bin diddigi da yin -hisabi-.
To shin zai yiwu ga wani mai mulki mai kiyayewa wanda ba ya sakaci da mafi ƙanƙantar mu'amalar ta mafi ƙasƙancin mutum ɗaya daga cikin talakawansa, a ce ba zai kiyaye kuma ya ajiye bayanan mafi girman ayyukan mafi girman talakawansa ba, kuma ba zai bi diddiginsu ba, kuma ba zai ba su kyakkyawan sakamako ko ya yi musu uƙuba ba?!kuma tun da waɗannan manyan suna aikata wasu abubuwa da suke taɓa buwayar wannan sarki da kishinsa, kuma jin-ƙansa bai yarda da su ba kwata-kwata, kuma shi ba ya yi musu uƙuba a nan, ashe kenan an jinkirta lamarin ne zuwa wata kotun babba.
[1]Haƙiƙa an yi bayanin wani ɓangare na ma'anonin da wannan misali yake nuni zuwa gare shi a "haƙiƙa ta bakwai", sai dai mu a nan muna cewa:haƙiƙa abin da babbar kyamara ta sarki ke nunawa kuma haƙiƙaninta shi ne Lauhul Mahafuzu,kuma an riga an tabbatar da samuwar Lauhul Mahafuzu a "kalma ta Ashirin da Shida" kamar haka:kamar dai yadda ƙananan katinan tantance mutane suke alamta samuwar wata matattara babba ta katunan tantance mutane, hakanan ƙananan takardun shaida suna nuni zuwa ga samuwar babban daftari, kuma ƙananan tsattsafar ruwa suna nuni zuwa ga maɓuɓɓuga babba ta ruwa, to hakanan ƙarfin ƙwaƙwalwar ‘yan’dam, da 'ya'yan itatuwa na bishiyoyi, da ƙwallayen 'ya'yan itacen da irinsu wanda suke kwatankwaci ne na katunan tantancewa ƙanana, kuma kamar Lauhul Mahafuzu ne ƙarami, su kuma kamar ƙananan ɗigo-ɗigo ne masu malala daga alƙalamin da ya yi rubutu a kan Lauhil Mahafuzu babba, lallai su suna alamta samuwar babbar ƙwaƙwalwa, da matattara (rajista) babba, da Lauhul Mahafuzu babba, kuma suna tabbatar da su,bil hasali ma su na nuna su, kuma suna bayyana su ga kaifafan hankula (mawallafi).


