MISALI NA BIYAR
NAVIGATION
9. Page
ambaton tausasan kyawunsa ɓoyayyu, ashe kenan yana da kamaloli da kyawu na ma'ana masu girma masu ban mamaki.
Ita kuwa kamala ɓoyayyiya wadda babu tawaya a cikinta to ana kwaɗayin shelanta ta ne a bainar masu kallo masu yabawa, masu nuna mamaki da ita masu cewa ما شاء اللهmasha Allah, shi kuwa kyawu ɓoyayye wanda ba shi da tamka to ya wajaba ya gani kuma a gan shi, a kalle shi kuma ya kalla, ma'ana ya ga kyawunsa ta hanya biyu, ta farkonsu ya ga kyawun kansa da kansa a cikin madubai mabambanta, hanya ta biyu ita ce ya ga kyawun kansa ta hanyar ganin masu kallo masu shauƙi zuwa gare shi, masu ganin kyawunsa masu mamakinsa.
Ma'ana shi yana kwaɗayin ya gani a gan shi yana nufin kallo na dindindin da nunawa ta har abada.
Sannan haƙiƙa wannan madauwamin kyawu yana lazamtar dawwamar samuwar masu shauƙi kuma masu kallo masu ganin kyawun;domin dawwamamman kyawu ba ya yarda da mai shauƙi mai gushewa,domin mai kallon da aka hukunta masa gushewa ba tare da dawowa ba soyayyarsa kan juye ta zama ƙiyayya da zarar ya hararo cewa shi gushewa zai yi, kuma mamakinsa da girmamawarsa kan koma wulaƙantawa; domin shi ɗan’adam mai yin gaba ne da abin da ya jahilta da kuma abin da hannunsa bai zai iya kaiwa kansa ba,sai dai kuma dukkaninsu za su yi ƙaura su bar waɗannan gidaje na saukar baƙi da sauri su faku, kuma cikin ƙiftawar ido su ga wata 'yar ƙyallawa ta haske daga waccan kamala da wannan kyawu, ko kuma a ce wata 'yar inuwa rarrauna ta su, sannan su tafi su bar su ba tare da sun ƙoshi da ganinsu ba, to su kenan masu ƙaura ne zuwa bigiren kallo madawwami.


