MISALI NA BIYU
NAVIGATION
6. Page
MISALI NA FARKO
Shin zai yiwu ga wata masarauta-musamman irin wannan masarauta katafariya-a ce babu kyakkyawan sakamako a cikinta ga masu biyayya da suke mata hidima hidama ƙayatacciya kuma suke aikata ayyuka na gari a cikinta, kuma zai yiwu a ce babu uƙuba a cikinta ga masu saɓo?! Kuma tun da kyakkyawan sakamakon da uƙubar abune da kusan babu shi a nan; to kenan a can ne ake da babbar kotu a wani gidan[1].
MISALI NA BIYU
Dubi tafiyar lamura da yanaye-yanaye da abubuwan da ke faruwa a nan,yadda a ke rarraba mafificin arziƙi kuma mafi kyawunsa ga kowa da kowa har mafi talaucinsu da rauninsu, da yadda a ke kulawa da marasa lafiya waɗanda ba su da mai karesu ko mai kulawa da su kyakkyawar kulawa, kuma ga waɗannan nau'o'in abinci daɗaɗa masu daɗi, da mazubai na alfarma, da lambobin yabo ababan tsarawa, da tufafi ababan yi wa ado,da liyafa ƙasaitacciya ta alfarma, kalli yadda kowa ke yin aikinsa cikin kyautatawa, in ban da wawaye sokwaye irinka, babu mai wuce iyakarsa daidai
lahira[1]
7. Page
da misalin ƙwayar zarra, mafi girman mutane yana aiwatar da aikinsa cikin ƙasƙantar da kai cikin matuƙar biyayya da tsoro da jin kwarjini, ashe kenan mamallakin wannan masarauta yana da karamci mai girma da rahama mai matuƙar yalwa, kuma yana da buwaya mai girma da daraja isasshiya da kishi maɗaukaki,kuma tare da cewa karamci na tare da ni'imtawa, rahama ba ta kasancewa ba tare da kyautatawa ba, buwaya tana janyo kishi, kuma daraja da kishi suna tabbatar da yin uƙuba ga wanda ya munana ladabi, ɗaya cikin dubu na abin da ya dace da waccan rahamar da wancan kishin ba sa bayyana a wannan masarauta, don haka sai azzalumi ya ci gaba da zama cikin buwayarsa, abin zalunta ya ci gaba da zama cikin ƙasƙancinsa har ƙarshen rayuwarsu, don haka lamarin ana jinkirta shi ne zuwa wata kotu babba.
MISALI NA UKU
Dubi yadda lamura ke tafiya cikin hikima maɗaukakiya da tsari da zubi mai matuƙar kyawu da ban ƙaye, da yadda a ke gudanar da mu'amaloli cikin adalci na haƙiƙa da ma'auni mai matuƙar taka-tsan-tsan mai tsantsancewa,to yayin da hikimar hukuma take wajabta tausasawa da kyautatawa zuwa ga masu fakewa zuwa ga mafaka ta kariyar masarauta, kuma adalci yake buƙatar kiyaye haƙƙoƙin talakawa, har a kiyayewa hukuma karamarta a kare muhibbar masarauta, sai dai ba a zartar da komai ba face ɗaya cikin dubu na abin da ya dace da waccan hikima da adalci, kuma mafi rinjayen wawaye irinka su sha ba tare da uƙuba ta hau kansu ba, kenan ana jinkirta lamarin ne zuwa wata kotun.


