MISALI NA FARKO

6. Page

MISALI NA FARKO

 

Shin zai yiwu ga wata masarauta-musamman irin wannan masarauta katafariya-a ce babu kyakkyawan sakamako a cikinta ga masu biyayya da suke mata hidima hidama ƙayatacciya kuma suke aikata ayyuka na gari a cikinta, kuma zai yiwu a ce babu uƙuba a cikinta ga masu saɓo?! Kuma tun da kyakkyawan sakamakon da uƙubar abune da kusan babu shi a nan; to kenan a can ne ake da babbar kotu a wani gidan[1].

                                                               

 

MISALI NA BIYU

 

Dubi tafiyar lamura da yanaye-yanaye da abubuwan da ke faruwa a nan,yadda a ke rarraba mafificin arziƙi kuma mafi kyawunsa ga kowa da kowa har mafi talaucinsu da rauninsu, da yadda a ke kulawa da marasa lafiya waɗanda ba su da mai karesu ko mai kulawa da su kyakkyawar kulawa, kuma ga waɗannan nau'o'in abinci daɗaɗa masu daɗi, da mazubai na alfarma, da lambobin yabo ababan tsarawa, da tufafi ababan yi wa ado,da liyafa ƙasaitacciya ta alfarma, kalli yadda kowa ke yin aikinsa cikin kyautatawa, in ban da wawaye sokwaye irinka, babu mai wuce iyakarsa daidai

lahira[1]