MISALI NA GOMA
NAVIGATION
19. Page
MISALI NA GOMA
Taho, domin yau ranar sallar kaka ce ta sarki[1], wasu sauye-sauye da canje-canje za su auku, kuma lamurra masu ban mamaki za su bayyana, to mutafi a wannan rana kyakkyawa daga cikin ranakun lokacin kaka zuwa waɗancan kwarurruka kwarra waɗanda aka ƙawata su da furanni masu kyawu, mu ɗan shaƙata, ga dai waɗannan
[1]Za ka ga alama manuniya ta wannan misali a cikin "haƙiƙa ta tara", domin misali ranar idi a nan tana nuni ne zuwa ga lokacin kaka, su kuwa kwarurruka kwarra masu furanni to su ne birbishin ƙasa a lokacin kaka, su kuwa fusakun talabijin da labulaye da abubuwan kallo masu caccanzawa suna nuni ne zuwa ga matakai na samammun abubuwa a lokacin kaka. Da gungu-gungun abubuwan samarwa a lokacin zafi da abubuwan ci waɗanda a kansu ne arziƙin dabbobi da mutane yake kewayawa waɗanda kuma mai samarwa mai iko ma'abocin girma maƙagi mai hikima ma'abocin kamala yake caccanza su daga farkon lokacin kaka zuwa ƙarshen lokacin zafi, kuma yake sabunta su da cikakkiyar rahama, kuma yake aiko su a jejjere wasu na bin wasu.(mawallafi).
20. Page
mutanan gari su ma suna zuwa su kansu zuwa wannan guri, kuma akwai wani lamari da yake kamar sihiri, domin dai ga gine-gine an rusa su, kuma take sun ruguje kuma sun koma wata kama da ban, kalli;wannan mu'ujiza ce, gine-ginen da aka rusa suka ruguje an sake gina su a nan take a nan, kamar ka ce wannan faƙo ya koma wani birnin mai ci gaba, kalli, ita tana bijiro da wata duniya mabambanciya a kowa ce awa kamar fuskar allon sinima, kuma tana fitowa cikn kama mabambanciya.
Ka zurfafa nazari cikin wannan; haƙiƙa a cikin waɗannan fuskoki na allon sinima na haƙiƙa masu cakuɗaɗɗun surori masu saurin wucewa masu yawa akwai tsaruwa mai ban ƙaye abar kyautata ƙirarta, ta yadda a ke sanya kowane abu a gurbinsa da ya dace da shi cikin tsantsancewa, kai hatta ma fuskar sinimar ta riyawa ba zai yiwu ta zama mai ban sha'awa mai ƙayatarwa kamar haka ba, kuma miliyoyin masu sihiri ƙwararru gogaggu ba za su iya aiwatar da waɗannan fasahohi da ƙirƙire-ƙirƙiren ba, kenan wancan sarki da ya ɓuya ga garemu yana da mu'ujizozi masu girma masu yawa.
21. Page
Ya kai wannan dolo, haƙiƙa kai kana cewa: "ta yaya za a ruguza wannan masarauta mai girma, kuma a sake gina ta a wani gurin da ban? To ga shi dai kai kana ganin Jujjuyawa lamura da sassauyawarsu da caccanjawarsu masu yawa suna faruwa a kowace awa kamar sassauyawar waɗancan gidaje da hankalinka ba ya karɓa, kuma yana bayyana daga waɗannan,haɗuwa da rabuwa,daga kuma waɗannan yanaye-yanaye cewa dukkan waɗannan haɗuwa da rabuwa da gine-gine da ruguje-ruguje masu sauri da ake ganin su,a cikinsu akwai wasu manufofi da ban waɗanda ba su ake nufi ba a kan kansu;domin a cikinawa ɗaya ta waɗannan haɗuwa a na kashe kwatankwacin abin da ake kashewa a shekara,don haka su ba komai ba ne face samfurori ,wannan sarki ne ke aikata wannan mu'ujiza, har a ɗauki hotunansu a tattara, a kiyaye sakamakonsu a taskace, kuma kamar yadda a ke kiyaye kowane abu a taskace shi a fagen atisaye da jarrabawa, kenan haka gudanar da tsare-tsare za ta ci gaba bisa wannan turba a matattara babba kuma a kan haka za ta gewaya, kuma za a bijiro da ita a wajen baje koli babba, ma'ana waɗannan yanaye-yananye masu gushewa na wucin gadi waɗanda ba masu tabbata ba, za su samar da surori matabbata da sakamako wanzajje, kenan to waɗannan bukukuwa ana yin su ne saboda wata babbar rabauta da kotu babba, da manufofi da ba mu san su ba.


