MISALI NA SHA BIYU

24. Page

MISALI NA SHA BIYU

 

Zo mu koma yanzu domin mu gana da shuwagabannin waɗannan jama'u da ofisa-ofisa na su, kuma mu kalli na'urorinsu da injinansu don mu ga shin an tanadi waɗannan na'urori da injina ne domin rayuwa a wani lokaci taƙaitacce a cikin wannan fage ne, ko kuwa an tanade su ne dominn katari da rabauta ta doguwar rayuwa a wani gurin daban, domin mu ba za mu iya kallon komai ba, ko mu iya ganin dukkan na'urorin da injinan, sai dai za mu iya duba katin tantancewa ne kawai na wannan ofisa da rajistarsa a matsayin samfuri, a dai cikin wannan kati akwai matsayin wannan ofisa, da matakin albashinsa da aikinsa da nauyin da ke kansa da kuma tsarin kai komo ɗinsa.

 

Duba, wannan matsayin ba wai an ba da shi ba ne saboda wasu 'yan kwanaki, sai dai saboda wani lokaci mai tsawo ƙwarai, kuma a cikin wannan kati an rubuta kwanan wata na karɓar albashinsa daga cikin taska keɓantacciya,sanin cewa wannan kwanan wata zai zo ne fa bayan zamani mai tsawo,kuma bayan ma an rufe wannan fage -na ɗaukar horo-, wannan aiki kuwa ba wai -zai yi shi ba ne- domin -amfanin- wannan fage na wucin gadi, sai dai an  ba shi ne saboda samun wata rabauta madawwamiya ta hanyar samun kusanci zuwa ga wannan sarki,su kuwa waɗannan abubuwa na wajibi da aka ɗora masa su ba zai yiwu su kasance saboda wata rayuwa ta 'yan kwanaki ba a wannan gida na saukar baƙi, sai dai su kasance saboda wata rayuwa ta rabauta mai tsawo, shi kuwa wannan tsari na aiki yana bayyana ne ƙarara a fayyace gaba ɗaya cewa shi mai wannan katin fayyacewar abin zaɓa ne domin tafiya zuwa wani gurin, kuma yana kai komo ne da yin aiki domin wata duniyar ta da ban.


25. Page

Dubi waɗannan rajistoci, a cikinsu akwai bayanin nauye-nauye da yadda ake amfani da injinan da na'urorin, to idan dai kuwa babu wani guri maɗaukaki na dindindin koma bayan wannan fagen shi kaɗai, to kuwa wannan rajista da kati ababan kyautatawa za su zama ba su da wata ma'ana kwata-kwata, kuma shi wannan ofisa abin ƙimantawa, kuma da wannan kwamanda abin karramawa, kuma shugaba abin darajtawa matsayinsa zai zube zuwa mafi ƙasƙanci daga matsayin dukkan 'yan ƙasa, kuma ya zama mafi taɓewar mutane, mafi gajiyawa da ƙasƙanci da bala'i da masifa a talauci da rauni, kuma ka kwatanta ragowar ɓangarorin ma kamar haka, kuma idan ka zurfafa nazari cikin kowane abu za ka ga cewa shi yana shaidawa cewa bayan wannan duniyar mai ƙarewa akwai wata duniyar wanzajjiya.

 


26. Page

Ke nan ya kai wannan aboki, haƙiƙa wannan masarauta ta wucin gadi kamar gona ce, kuma farfajiya ce ta koyo da horarwa, kuma kasuwa ce, don haka ba shakka bayanta wata kotu babba da rabauta mai girma za su zo bayanta, to idan ka musanta haka to zai zame maka tilas ka musanta dukkan katuna na tantance mutane da rajista-rajista da injina da na'urori da tsarurrukan aiki da suke wajen dukkan ofisa-ofisa, kai (za ka yi musun) dukkan tsarurruka ma a wannan masarauta ko ma muce ita hukumar kanta, kuma ya wajaba ma ka yi inkarin samuwar tsare-tsaren aiwatarwa zartattu, a sannan kuwa ba za a kira ka mutum mai ji a ransa mai fahimta ba, kuma za ka zama mafi tsananin wauta da dolanci daga Sufasɗawa.

 

Kuma kul ka zaci cewa alamomin sassauyawar wannan masarauta sun taƙaita ne ko sun tsaya kawai kan waɗannan misalai sha biyu, a'a akwai ma wasu alamomin da ba su da iyaka ko adadi, waɗanda suke nuna cewa wannan masarauta mai canzawa mara tabbata za a juya ta zuwa wata masarauta matabbaciya da ba za ta gushe ba, kuma akwai wasu isharori da alamomi marasa iyaka da adadi da suke nuni zuwa cewa waɗannan 'yan ƙasa da mazauna za a ɗauke su daga waɗannan gidajen saukar baƙi masu ƙarewa, a cira su zuwa matabbata dauwamammiya ta masarautar.

 


27. Page

Zo na nuna maka wata hujjar daban mafi ƙarfi daga misalannan sha biyu, duba, haƙiƙa manzo mafi karamci, ma'abocin lambar yabo mai girma wanda muka gan shi a tsibirin nan da can yana isar da saƙo a tsakanin jama'ar nan mai girma waɗanda muke hango su daga nesa, taho mu je mu saurare shi, to kalli, haƙiƙa wannan manzo mafi karamci mai tushen haske yana isarwa ga 'yan ƙasa doka mafi girma wadda aka rataye a sama, kuma yana cewa: ku shirya ku kintsa, za ku ƙaura i zuwa wata masarauta daban dawwamammiya, ita masarauta ce wadda masarautarmu wannan ba ta fi a ce ɗakin kurkuku ne game da ita ba, to idan kun saurari wannan doka da kyau da mai da hankali, kuma kun yi biyayya kun aiwatar da ita, to da sannu za ku ciru zuwa matabbatar masarautar sarkinmu, kuma da sannu za ku sami rahamarsa da kyautaye-kyautayensa, in kuwa kun saɓa ba ku saurare shi ba to da sannu za a tafi da ku zuwa ɗakunan kurkuku masu matuƙar ban tsoro.

 

Haƙiƙa shi yana yin sharhi kuma yana isarwa ga mahalarta irin waɗannan lamura,kuma haƙiƙa kai kana ganin cewa a cikin wannan doka maɗaukakiya akwai wani hatimi gagara koyo da ba za a taɓa iya kwaikwayansa ba ta kowace fuska, kuma kowa ya sani tabbas,in ban da dolaye irinka, cewa wannan doka doka ce ta wann sarki kuma bayani ne nasa, kuma cewa wannan manzo mafi karamci yana da wasu lambobin yabo ta yadda kowa zai fahimta, in ban da makafi kamarka, cewa wannan mutum shi mai isarwa ne mai matuƙar gaskiya ga umarce-umarcen sarki.

 


28. Page

To bayin Allah, yanzu zai yiwu ga wannan mas'ala-wato mas'alar canza wannan masarauta da wannan manzo mafi karamci yake da'awarta kuma yake isar da ita tare da wannan bayani da wancan saƙo mafiya girma da dukkan ƙarfinsu-shin zai yi wu a yi musunta?!

Faufau, haƙiƙa su ba za ta karɓi musantawa ba, sai dai fa idan za ka musa duk abin da kake gani ko kallo.

To ya kai wannan aboki, yanzu kuma damarkace, don haka ka faɗi abin da ka ga dama.

To ni mai zan iya cewa, shin za a iya faɗar wani abu bayan wannan, kuma shin za a iya yin kokwanton samuwar rana a tsakiyar yini, kuma ni dai bani da abin da zan ce face: dukkan yabo ya tabbata ga Allah, kuma dubu-dubun godiya na gare shi, haƙiƙa na kuɓuta daga mulkin mallaka na zaton riyawa da son zuciya, da kuma ribatar zuciya da son zuciya, kuma na tsira daga kurkuku-kurkuku da ɗakunan kurkuku na har abada, kuma na gasgata na ba da gaskiya cewa akwai wasu gidaje na rabauta daban a wajen sarki mamallaki koma bayan wannan gidan saukar baƙin mai tambal-tambal mara tabbata ba, kuma mu ababan zaɓe ne domin tafiya can.


29. Page

Haƙiƙa a nan wannan labari na kwaikwayawa wanda ake kinaya da shi game da tashin Alƙiyama da Lahira, da kuma bayani game da su ya tiƙe, yanzu kuma za mu tafi zuwa haƙiƙa maɗaukakiya da datarwar Ubangiji, kuma za mu bayyana "Haƙiƙu sha biyu" masu goyan bayan juna tare da gabatarwa, waɗanda suke daurantar "Misali sha biyu" da aka ambata a baya.

 

GABATARWA

 

Wasu daga cikin isharori da aka yi suna nuni ne zuwa wasu daga cikin mas'aloli da aka fayyace a wasu guraren da ban, ma'ana a cikin kalma ta "sha tara" da ta"ashirin da biyu" da kuma ta "ashirin da shida".