MISALI NA SHA ƊAYA
NAVIGATION
22. Page
MISALI NA SHA ƊAYA
Taho, ya kai wannan aboki mai taurin kai mu hau wani jirgin sama ko jirgin ƙasa da ya nufi gabas ko yamma, ma’ana zuwa zamanin da ya wuce ko zamani mai zuwa, don mu ga kuma mu kallaci kowane nau'i na mu'ujizozin da wancan sarki ma'abocin mu'ujizozi yake bayyanawa a wasu guraren daban.
Ka ga kalli, haƙiƙa abubuwan mamaki da muka gan su a baya kamar gida da fage da guraren baje koli ana ganin su a kowane waje, kuma kowane daga cikinsu yana da abin da ya banbanta da shi daga sauran ta fuskar samarwa da kamanni, kuma ka zurfafa kallo cikin wannan lamari;akwai tsaruwar hikima maimatuƙar ƙayatarwa da ke cikinsa ta isa abin mamaki, hakanan isharori na kulawar ubangiji mabayyana, da alamomi na adalci maɗaukaka,da sakamako na rahama mayalwaciya da suke bayyana a waɗancan gidaje waɗanda ba masu tabbata ba, da fagage waɗanda ba masu dawwama ba, da guraren baje-koli waɗanda ba masu wanzuwa ba, kuma duk wanda bai rasa basirarsa ba zai gane bisa yaƙini cewa ba zai yiwu ba a ce akwai wata hikima mafi cika daga hikimarsa, da wata kulawa mafi kyawu daga kulawarSa, da rahama mafi gamewa daga rahamarSa, da adalci mafi girma daga adalcinSa, kai ba zai yiwu ba ne ma a ce an yi tunanin hakan, kuma sanannen abu ne cewa wannan masarauta wadda ba matabbaciya ba ce ba ta iya zama mabayyana ga haƙiƙoƙin hikima da kulawa da rahama da adalci, to kuwa idan dai a cikin hurumin mulkinsa ba za a sami gidaje madauwama ba, da gurare maɗaukaka, da mazaunai tabbatattu, da masaukai wanzazzu, da 'yan gari da mazauna da talakawa masu jin daɗin rayuwa
23. Page
da waɗannan haƙiƙoƙi suke bayyana a kansu-a ɗauka ma haka ne kamar yadda kai kake riyawa – kuma idan ba su kasance za su bayyana a wani gurin da ban ba, to a sannan ne ya wajaba mu musa wannan hikima da mu ke ganinta da idanunmu ƙaru-ƙuru, kuma wannan kulawa da muke kallonta, da wannan rahama da muke taɓata da hannayenmu, da kuma wannan adalci da alamominsa da isharorinsa ƙarfafa ƙwarai suke bayyana, ya wajaba a musanta duk waɗannan da irin wautar da ake musanta fitowar ranar da muke ganin haskenta a tsakiyar yini, kuma ya wajaba mu yarda cewa wanda yake aiwatar da waɗannan gudanar da tsare-tsare masu hikima, da ayyuka masu karamci, da kyautaye-kyautayenSa masu cike da rahama waɗanda muke ganinsu – ya tsarkaka ya tsarkaka – a ce shi mai wargi ne wawa ne, ko a ce azzalumi mai yaudara, wannan – idan an ce haka – yana nufin haƙiƙoƙi su juye su zama kishiyoyinsu, alhali kuwa juyewar haƙiƙoƙi zuwa kishiyoyinsu abune mara yiwuwa, kuma mara saɓuwa bisa haɗuwar maganar dukkan masu hankali, in banda Sufasɗawa wawaye waɗanda suke inkarin samuwar komai.
Kenan lallai akwai wasu gidajena daban banda waɗannan gidajen, kuma a cikinsu akwai kotu babba da gida na adalci maɗaukaki, da gidan karamci babba ta inda wannan rahama da hikima da kulawa da adalci za su bayyana su fito ƙarara a cikinsu.


