MISALI NA SHIDA
NAVIGATION
10. Page
MISALI NA BIYAR
Yi duba, haƙiƙa yana bayyana cikin waɗannan lamura cewa wannan sarki da ba shi da tamka yana da tausayi da rahama mai girma, domin shi yana agazar duk wanda musiba ta same shi, kuma yana amsa dukkan roƙo da buƙata, har ta kai shi idan ya ga mafi ƙanƙantar buƙata ta mafi ƙasƙancin mutum daga talakawansa sai ya biya masa ita da tausayi da jin-ƙai, kuma idan ƙafar wata tinkiya ta wani makiyayi ta ɗan ji ciwo sai ya aiko magani ko likitan dabbobi.
Biyo ni mu tafi zuwa wannan tsibiri domin a cikinsa akwai taro mai girma, domin ɗaukacin manyan mutane masu alfarma na masarautar sun taru, kalli, haƙiƙa ga wani jakada mafi girma yana ɗauke da wata lambar yabo maɗaukakiya ƙwarai, yana jawabi yana roƙon sarkinsa mai jin ƙai mai rahama, kuma yana roƙonsa wasu lamura, kuma daukacin mazauna da mutanan masarautar suna cewa: "hakan ne;haka ne; mu ma haka muna roƙonka muna nema", kuma suna gasgata shi suna mara masa baya.
11. Page
Yanzu saurara, haƙiƙa masoyin Sarkin yana cewa: "ya sarkinmu wanda yake tsirar da mu ya raine mu da ni'imarsa, ka nuna mana tuwasu da maɓuɓɓugan surori da inuwoyi waɗanda ka nuna mana, kuma ka ɗauke mu zuwa matabbatar masarautarKa, kuma kada ka hallakar da mu a cikin waɗannan saharori da zazozi, ka ɗauke mu zuwa gadon sarautarka kuma ka jiƙanmu, ka ciyar da mu ni'imomi masu daɗi acan, waɗanda ka ɗanɗana mana su a nan,kada ka azabtar da mu da gushewa da nisantawa daga gare ka, kada ka bar mu, mu talakawanka masushauƙi zuwa gare ka, masu gode maka masu biyayya gare ka, ababen bazamawa da watangaririya, kada ka rasar da mu",ya ci gaba da kamun ƙafa, yana mai ahi zuwa gare shi da yawa, kai kuma kana jin haka, to jama'a yanzu zai yiwu a ce wannan sarki mai jin ƙai mai rahama irin wannan a ce ya biyawa mafi ƙasƙancin mutum wata buƙatarsa cikin himmatuwa, sannan a ce ba zai biya mafi girman abin nema na mafi soyuwar jakada mai girma a wajansa ba, tare da cewa abin neman wannan masoyi shi ne abin neman kowa da kowa, kuma abin yardar sarkin da kuma ya dace da rahamarsa da adalcinsa, kuma abune mai sauƙi gurin wannan sarki,kuma ba zai nauyaye shi ba,kamar yadda samar da guraren shaƙatawa na wucin gadi ba zai nauyaye shi ba a wannan gida na saukar baƙi, sai dai ma a ce shi mafi sauƙi ne a gare shi?!
12. Page
Kuma tun da yake shi ya ƙirƙiri wannan masarauta kuma ya yi mata irin wannan ɗawainiya wajen samar mata da ababan more rayuwa cikin waɗannan guraran shaƙatawa da za su wanzu na tsawon kwana biyar ko shida domin ya nuna kuma ya bayyana samfura na taskokinsa da kamalolinsa da ƙirƙire-ƙirƙirensa na haƙiƙa na ɗan tsawon wasu 'yan kwanaki, to lallai ba shakka a can matabbatar masarautarsa zai buɗe wasu guraran shaƙatarwar da za su yi matuƙar burge hankula kuma su yi matuƙar ba su mamaki,kuma a cikinsu zai baje kolin taskokinsa da kamalolinsa da ƙirƙire-ƙirƙirensa na haƙiƙa,a she kenan waɗannan da suke cikin wannan gidan jarrabawa ba sakakku ba ne masu 'yanci,a maimakon haka fadojin farin ciki da kuma gidajen kaso suna jiransu.
MISALI NA SHIDA
Zo ka duba,haƙiƙa waɗannan jiragen sama da jiragen ƙasa da tanade-tanade da sito-sito da guraren baje koli da tsare-tsare cikakku masu girma suna nuna cewa bayan wannan katanga akwai wata masarauta mai girma[1] da ta ke hukunci, ita ko masarauta
[1] kamar yadda wata babbar runduna a fagen atisaye a ɗaukacinta ta yi kama da wani daji mai ƙayoyi bayan ta amsa umarnin "ku ɗauki makamai ku kuma shirya majaujawunku" kamar yadda yake a ƙa'idojin yaƙi, kuma kamar yadda shi sansanin a ranar salla yayin faretin soja, ya yi kama da wani lambu mai ado da furanninsa masu launi-launi suka bubbuɗe bayan sun amsa umarnin da yake cewa:"ku sassaka tufafinku na aiki,kuma ku rarrataya lambobin yabonku", to haka ma wasu sassa na tsirrai waɗanda ba su da hankali da tsinkaye waɗanda suma nau'i ne daga nau'o'in rundunonin sarkin na tun fil azal marasa iyaka, kamar dai mala'iku da aljanu da mutane da dabbobi a fagen bayan ƙasa,yayin da suka karɓi umarnin Ubangiji da yake cewa:"ku harhaɗa makamanku da na'urorinku" domin ba da kariya da umarnin"kasance sai ya kasance" cikin jihadin kare rayuwa, haƙiƙa ƙasa baki ɗayanta tana kama da wani sansani na wata runduna babba wadda sojojinta suka harhaɗa masunsu yayinda dukkan bishiyu da tsirrai masu ƙayoyi suke harhaɗa masunsu, kuma tun da yake kowane yini da kowane mako na lokacin kaka shi kamar wata ranar salla ce ga watajama’a dagajama’u na tsirrai,to kowane jama’a daga cikinsu suna baje kolin lambobin yabo masu dajiya da aka rataya musu ne a yanayin da ya yi kama da fareti na hukuma a gaban mahalarta na sarkin tun fil azal tare da shaidawarsa da ya ɗora musu nauyinta,kuma suka rungumi wannan yanayi na baje kolin kyaututtuka masu kyau da sarkinsu kuma mamallakinsu ya yi musu kyautarsu, kamar dai ka ce dukkan bishiyoyi da tsirrai suna ji kuma suna biyayya ga umarnin Ubangiji mai cewa: "Ku rataya ƙere-ƙeren Ubangiji ababan yi wa ado, da lambobin yabo na zubin halittar Ubangiji waɗanda su ne furanni da 'ya'yan itatuwan, kuma ku bubbuɗe furannin", yayin ne bayan ƙasa kuma a ranar sallah mai girma zai yi kama da wani sansani da yake ƙyalƙyali da walwali da tufafin aiki ababan yi wa ado da lambobin yabo ababan dajewa a cikin wani fareti na hukuma ƙayatace mai ban sha'awa.
Babu shakka waɗannan ƙawace-ƙawace da tanade-tanade masu cike da hikima da dajewa da tsaruwa irin haka suna bayyanawa da fayyacewa ga waɗanda ba makafi ba ne cewa hakan na faruwa ne da umarnin wani sarki mai iko wanda ikonsa ba shi da iyaka, kuma mai mulki mai hikima wanda hikimarsa ba ta da iyaka.(mawallafi).
13. Page
irin wannan tana buƙatar talakawa da za su dace da ita, a yanayin da ake ciki kuwa kai kana gani cewa dukkan waɗannan talakawa sun taru a wannan gida na saukar baƙi, wannan gida kuwa ana cika shi kuma a na yashe shi a kowace rana,kuma dukkan talakawan sun taru a wannan fili na jarrabawa saboda atisaye, shi kuwa filin ana canza shi kowace awa, kuma dukkan talakawan suna wanzuwa na 'yan wasu daƙiƙoƙi a wannan fili na baje koli, kuma a cikinsa suna kallon samfurori na kyautaye-kyautayen sarkin masu ƙima,da tsarabe-tsaraben ababen ƙerawarsa masu ban ƙaye da abubuwan mamakinsu, shi kuwa birnin ana sauya shi ne kowace daƙiƙa, kuma waɗanda suka bar shi ba za su taɓa komowa cikinsa ba, mai gabatowa zuwa gare shi mai tafiya ne ya bar shi.
To wannan hali da yanayi suna nuna cewa lallai bayan wannan gidan na saukar baƙi da wannan fili da waɗannan guraren baje koli akwai wasu fadoji madauwama, da gidaje masu ci gaba madawwama, da lambuna da taskoki waɗanda aka cika su da tuwasun abubuwa tatattu maɗaukaka na waɗannan samfura da surori, ashe ke nan, wannan kai kawo da ƙwazo da ake yi a nan, duk domin a samu sakamako ne a can, shi yana sanya su aiki ne a nan domin ya ba su ladansu a can, don haka kowa zai samu rabauta ne a can gwargwadon irin tanadinsa.


