MISALI NA TAKWAS

15. Page

suna tantance kowanne abu har mafi ƙanƙantar ayyuka da mafi sauƙin abubuwa masu faruwa.

 

Kalli,an kafa wata kyamara babba[1] a kan wancan babban dutse, wadda ta ke ta musamman ce wajen wannan sarki, tana ɗaukar dukkan abin da yake gudana a dukkan waɗannan gurare, ashe kenan shi ya yi umarni da a rubuta a tantance dukkan mu'amaloli da lamura da suke gudana a masarautarsa, wannan kuwa na nufin cewa wannan sarki mai girma ya yi umarni da a rubuta dukkan abubuwan da suke faruwa kuma a ɗau hotunansu, to lallai ba makawa wannan kiyaye bayanai cikin matuƙar tantancewa ana yin sa ne don bin diddigi da yin -hisabi-.

 

To shin zai yiwu ga wani mai mulki mai kiyayewa wanda ba ya sakaci da mafi ƙanƙantar mu'amalar ta mafi ƙasƙancin mutum ɗaya daga cikin talakawansa, a ce ba zai kiyaye kuma ya ajiye bayanan mafi girman ayyukan mafi girman talakawansa ba, kuma ba zai bi diddiginsu ba, kuma ba zai ba su kyakkyawan sakamako ko ya yi musu uƙuba ba?!kuma tun da waɗannan manyan suna aikata wasu abubuwa da suke taɓa buwayar wannan sarki da kishinsa, kuma jin-ƙansa bai yarda da su ba kwata-kwata, kuma shi ba ya yi musu uƙuba a nan, ashe kenan an jinkirta lamarin ne zuwa wata kotun babba.

 


[1]Haƙiƙa an yi bayanin wani ɓangare na ma'anonin da wannan misali yake nuni zuwa gare shi a "haƙiƙa ta bakwai", sai dai mu a nan muna cewa:haƙiƙa abin da babbar kyamara ta sarki ke nunawa kuma haƙiƙaninta shi ne Lauhul Mahafuzu,kuma an riga an tabbatar da samuwar Lauhul Mahafuzu a "kalma ta Ashirin da Shida" kamar haka:kamar dai yadda ƙananan katinan tantance mutane suke alamta samuwar wata matattara babba ta katunan tantance mutane, hakanan ƙananan takardun shaida suna nuni zuwa ga samuwar babban daftari, kuma ƙananan tsattsafar ruwa suna nuni zuwa ga maɓuɓɓuga babba ta ruwa, to hakanan ƙarfin ƙwaƙwalwar ‘yan’dam, da 'ya'yan itatuwa na bishiyoyi, da ƙwallayen 'ya'yan itacen da irinsu wanda suke kwatankwaci ne na katunan tantancewa ƙanana, kuma kamar Lauhul Mahafuzu ne ƙarami, su kuma kamar ƙananan ɗigo-ɗigo ne masu malala daga alƙalamin da ya yi rubutu a kan Lauhil Mahafuzu babba, lallai su suna alamta samuwar babbar ƙwaƙwalwa, da matattara (rajista) babba, da Lauhul Mahafuzu babba, kuma suna tabbatar da su,bil hasali ma su na nuna su, kuma suna bayyana su ga kaifafan hankula (mawallafi).




16. Page

MISALI NA TAKWAS

 

Zo, in karanta maka waɗannan bayanai da waɗannan umarce-umarce da suka zo daga wajen wancan sarki, duba, haƙiƙa shi yana maimata alƙawarinsa, kuma yana yin alƙawari da tsanani, yana cewa: "zan ɗauke ku zuwa matabbatar masarautata, kuma zan sanya masu biyayya cikin rabauta, kuma zan jefa masu saɓo cikin kurkuku, a wannan lokacin ne zan rusa duniya, kuma zan fari wata masarauta da wani gida sababbi, da za su ƙunshi fadoji madauwama da kurkuku-kurkuku na dindindin".

 

Sannan kuma lamuran da ya yi alƙawarinsu sauƙaƙa ne masu sauƙi a gare shi, kuma suna da matuƙar muhimmanci ga talakawansa, shi kuwa saɓa alƙawari abu ne da ya ci karo da buwayar ikonsa kwata-kwata.


17. Page

Kalli ya kai wannan dolo, haƙiƙa kai kana gasgata maƙaryacin ruɗaninka, da hankalinka mai tamɓele,da zuciyarka mayaudariya, kuma kana ƙaryata wanda ba ya matsuwa ko ya buƙatuwa zuwa saɓa alƙawari ko saɓani ta kowace fuska,kuma wanda saɓa alƙawari ba ya dacewa da buwayarsa da karamarsa har abada,wanda kuma duk bayyanannun lamura ke shaidawa a bisa gaskiyarsa, lallai babu shakka kai ka cancanci uƙuba mai tsanani,misalinka dai kamar matafiyi ne da yake runtse idanunsa ga barin hasken rana, yana kallon abin da ƙwaƙwalwarsa ke riya masa, kuma yake so ya haskaka hanyarsa mai tsoratarwa mai razanarwa da hasken fitilar da yake riya ta a cikin ƙwaƙwalwarsa, kamar dai yadda maƙesuwa[1] ta ke yi.

 

Kuma tun da yake dai ya yi alƙawari, to ba shakka shi zai cika alƙawarinsa, kuma cika alƙawarinsa abune mai sauƙi a gare shi, kuma abune na ba makawa garemu da ma kowane abu, kuma yana daga muhimman abubuwan da suke maɗanfara gare shi, kuma maɗamfara ga masarautarsa.

 

Kenan lallai akwai wata kotu babba da kuma rabauta mafi girma.

 


[1]Wutar-yola