MISALI NA TARA
NAVIGATION
18. Page
MISALI NA TARA
Zo ka kalli wasu daga cikin shuwagabannin[1] waɗannan gundumomi da jama'u, domin kowanne daga cikinsu yana da wata wayar tangaraho tasa ta musamman da yake samun damar ganawa da sarkin da ita kai tsaye, kai ƙarewa ma dai ga wasu daga cikinsu sun hallara gaba gare shi a halararsa.
Me suke cewa ne? Haƙiƙa su suna ba da labari bisa haɗuwar maganarsu cewa wannan sarki ya tanadi wani gida ƙayatacce, da kuma wani mai ban tsoro don kyakkyawan sakamako da kuma uƙuba, haƙiƙa shi yana yin alƙawari alƙawari mai ƙarfi, kuma yana yin alƙawari da tsanani, kuma ya tsarkaka da buwayarsa da jalalarsa ga barin saɓa alƙawari, don haka ba ya karɓar ƙasƙanci ta kowace fuska, alhali su waɗannan masu ba da labari suna ba da labarai masu yawa da suka kai matakin ruwan dare gama duniya kuma tare da haɗuwar maganarsu wadda ta kai ƙarfin ijma'i cewa matabbatar wannan masarauta mai girma-wadda ake ganin wasu daga cikin gurabanta kuma ake kallonsu- shi yana cikin wata masarautar daban mai nisa, don haka gine-gine a wannan fage na jarrabawa na wucin gadi ne, sannan a juya su zuwa wasu fadoji na dindindin, waɗannan gurare za a sauya su;domin wannan masarauta mai girma madauwamiya wadda ba ta gushewa, kuma wadda girmanta ke bayyana ya fito daga gurabanta, ba ta tsayawa ita kuma ba ta dawwama bisa irin waɗannan lamura masu gushewa marasa dawwama marasa tabbata marasa muhimmanci, masu canzawa masu tawaya marasa cika waɗanda ba su da wanzuwa, kenan ita abar tsayarwa ce bisa wasu lamura da suka dace da ita, madawwama, matabbata masu zarcewa, cikakku masu ban ƙaye babu gushewa gare su, kenan akwai wasu gidaje daban, kuma babu makawa sai an tafi zuwa waccan matabbata.
[1]Haƙiƙa ma'anonin da wannan misali ke tabbatar da su za su bayyana a cikin "haƙiƙa ta takwas", ga misali:su shuwagabannin gundumomi a cikin wannan misali suna nuni ne zuwa ga annabawa da waliyyai,shi kuwa tangarahon wata dangantaka ce ta ubangijintaka da ta fara daga zuciya wadda ita ce gurin da wahayi yake sauka kuma ilhama ta ke bayyana, don haka zuciya ita ce kwatankwacin kan wannan tangarahon da kuma bututun jinsa (mawallafi) .


