Nuƙuɗa ta biyu

118. Page

Nuƙuɗa ta biyu: Tana bayyana hujja ɗaya daga hujjojin haƙiƙar tashin Alƙiyama marasa iyaka da take tsattsafowa daga taƙaitattun Shaidodin da suka samo asali daga wasu rukunan imanin.

 

Hakan kuwa ya kasance ne saboda cewa dukkan mu’ujizozin Shugabanmu Muhammadu-Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi-waɗanda suke nuni ga manzancinsa, da dukkan dalilan annabcinsa, da dukkan hujjojin da suke nuni  a bisa gaskiyarsa da cancantarsa dukkaninsu-kuma a ɗaukacinsu-suna shaidawa a bisa tabbatar haƙiƙar tashin Alƙiyama kuma suna tabbatar da ita; domin dukkan batutuwan wannan manzo a cikin dukkan rayuwarsa sun mai da hankali ne ga tashin Alƙiyama, wannan bayan tauhidi kenan, kuma cewa dukkan mu’ujizozinsa da hujjojinsa da suke gasgata dukkan annabawa kuma suke sanya mutane su gasgata su suna shaidawa da dai wannan haƙiƙa.

 

Kuma shaidawarsa da yake cewa وكتبهda Littattafansa wadda take ɗaukaka shaidawar da take zuwa bayan Kalmarورسلهda manzanninsazuwa matakin abin da kowa ya sani ita ma tana shaidawa da wannan haƙiƙar da kanta; dalili kuwa shi ne cewa dukkan mu’ujizozin Alƙur’ani mai gajiyarwa a bayaninsa da farko, da haƙiƙoƙinsa da hujjojinsa da suke tabbatar da cancantarsa dukkaninsu kuma a ɗaukacinsu suna shaidawa bisa tabbatar haƙiƙar tashin Alƙiyama da aukuwarta kuma suna tabbatar da ita; domin sulusin Alƙur’ani kusan yana maka Magana ne a kan tashin Alƙiyama, kuma ayoyin Tashin Alƙiyama masu ƙarfi suna zuwa a farkon mafi yawancin surori gajeru, kuma Alƙur’ani da dubban ayoyinsa yana ba da labari ƙarara da nuni game da ita dai wannan haƙiƙa kuma yana tabbatar da ita kuma yana bayyana ta.


119. Page

Ga misali: Haƙiƙa Shi yana nuni a farkon surori talatin ko arba’in zuwa cewa haƙiƙar tashin Alƙiyama itace-da dukkan tabbacinta-haƙiƙa mafi muhimmanci a tsakanin haƙiƙoƙin halitta, kuma cewa ita haƙiƙa ce wajiba, wannan kuwa ya zo a irin surorin

[1]إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ

[2]يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ

إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا[3]

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتۡ

[4]

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ

[5]

عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ

[6]


[1]{Idan rana aka shafe haskenta}

[2]{Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku.Lalle ne girgizar ƙasa ta tsayuwar Alƙiyama wata aba ce mai girma}

[3]{Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta}

[4]{Idan sama ta tsage}

[5]{Idan sama ta kece}

[6]{A kan me suke tambayar juna}




120. Page

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَة[1]ِ




Kuma yana bayyana dalilai nau’i-nau’i ga waccan haƙiƙa a cikin wasu ayoyin daban kuma yana gamsarwa da su.

 

To ya jama’a!Shin akwai wata yiwuwa ta kowace fuska daga fuskoki na imani da tashin Alƙiyama ya zama ƙarya ne-wanda yake bayyana kamar rana da dubban shaidu da da’awoyi-kamar wanda ambatonsa ya gabata-a cikin wani littafi wanda ishara ɗaya daga aya ɗaya daga cikinsa za ta samar da haƙiƙoƙi na ilimi da na halittar duniya masu yawa a cikin iliman musulunci a gaban idanuwanmu.

 

Shin hakan ba zai zama kamar inkarin samuwar rana ba ne, ko ko a ce kamar faɗar cewa babu duniya ba ne?!shin hakan ba zai zama abu mara yiwuwa ba kuma ƙarya sau ɗari?

 

Kuma ya jama’a shin abu ne mai yiwuwa ta ko wadda fuska daga fuskoki a ƙaryata dubban maganganu da alƙawarurrukan alherai da alƙawarurrukan narko na wani sarki mai matuƙar kwarjini da buwaya a yayin da wata runduna cikakkiya ta ke rawar jiki kuma wani lokaci ta ke yaƙi domin kada wata ishara ɗaya ta wannan sarkin ta zama ƙarya ce? To shin abu ne mai yiwuwa a ce dubban maganganunsa da alƙawuransa da barazanarsa su zama ba na haƙiƙa ba ne?

 

Kuma idan ishara ɗaya ta wannan sarkin na ma’ana ma’abocin sha’ani da ya mamaye[1] abin da ba shi da iyaka na ruhi-ruhi da hankula da zukata da rayuka a cikin kewayen gaskiya da haƙiƙa, kuma ya raine su ya gudanar da su tsawon ƙarni sha uku ba tare da yankewa ba ta isa ta tabbatar da haƙiƙa irin wannan, to ya jama’a!yanzu lamarin ba ya wajabta azabar Jahannama ga wawa jahilin da bai san wannan haƙiƙar ba bayan -wancan sarki-ya bayyana ta kuma ya tabbatar da ita da dubban bayanai ƙarara?! Yanzu wannan ba zai zama shi ne ainihin adalci ba?

 

Sannan bayanin dukkanin takardu saukakku daga sama da littattafai masu tsarki da aka saukar daga sama waɗanda suke yin hukunci bisa wani zamani daga zamunna, kuma suka taka rawa daidai da lokacinsu da zamaninsu, tare da karɓar wannan haƙiƙar karɓa mai yanke shakku ;ma’ana haƙiƙar tashin Alƙiyama wadda Alƙur’ani ya bayyana ta ya tabbatar da ita dalla-dalla tare da bayanai masu fayyacewa da maimaituwa, Alƙur’anin da ya mamaye dukkan zamani mai zuwa da ma dukkan zamuna ɗaukacinsu, abin da mu ke cewa shi ne haƙiƙa da’awoyinsu da tabbatarwarsu ga wannan haƙiƙoƙi ta hanya ƙaƙƙarfa, tare da bayaninsu ba tare da

[1]Ya mallake.




121. Page

yin dalla-dalla ba, cikin taƙaicewa, da kuma kangewa, lallai yana gasgata da’awar Alƙur’ani da dubban sanya hannu na amincewa.

 

A wannan gaɓar ne dangane da wannan bincike za mu shigar da shaidar ragowar rukunan, musamman ma shaidar rukuninالإيمان بالرسل و الكتبBa da gaskiya da manzanni da littattafai cikin rukuninالإيمان باليوم الآخرImani da ranar Lahira, wanda aka ambata a ƙarshen “Risalatul Munaajaat” -Risalar Ganawa- , wadda ita hujja ce daga hujjojin tashin AlƘiyama wadda aka ambata a cikin misalin ganawa, ita kuwa mai ƙarfi ce ƙwarai, kuma a taƙaice ta ke, kuma tana gusar da dukkan ruɗani, za mu kimsa ta a nan kamar yadda ta ke.

 

Haƙiƙa a cikin munajantin ya faɗakamar haka:

 

Ya Ubangijina mai jin ƙai, haƙiƙa na fahimta ta hanyar koyarwar manzo mafi karamci da kuma karantarwar Alƙur’ani mai hikima cewa dukkan littattafai masu tsarki da annabawa, wanda yake a kan gabansu Alƙur’ani da Manzo mafi karamci tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suna shaidawa kuma suna shiryarwa kuma suna nuni da ijma’i da haɗuwar kan maganarsu zuwa cewa tajallolin sunayen jalala da jamala da ake ganin samfuransu a dukkan sassa a cikin wannan duniya za su ci gaba cikin abadar abadodi da yanayi mafi bayyana kuma mafi haskakawa, kuma sun yi nuni zuwa cewa kyautaye-kyautayenka da a ke gani a cikin wannan duniya wadda tajallolinnta suke ƙarewa,da samfuranta da suke cike da jin ƙai za su kasance wanzazzu, kuma za su ci gaba a gidan rabauta cikin sura mafi ƙayatarwa, kuma suna nuni zuwa cewa masu shauƙantuwa da suke kallon waccan kyautatawa cikin morewa, kuma suke abokantakarta cikin soyayya a cikin wannan rayuwa taduniya gajeriya, za su abokancetakuma a duniya ta har abada, kuma za su kasance tare da ita.


122. Page

Sannan, haƙiƙa dukkan annabawa waɗanda su ne ma’abota ruhi-ruhi na haske-kuma a kan gabansu shi ne manzo mafi karamci tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Alƙur’aninKa mai hikima-suna masu dogaro kan ɗaruruwan mu’ujizozinsu masu matuƙar ban mamaki da ayoyinsu masu yanke shakku, kuma cewa dukkan waliyyai waɗanda su ne ƙuɗubai na zuciyoyi ababan haskakawa, kuma cewa dukkan siddiƙai waɗanda su ne ma’adanar hankula masu ketawa cikin sirrukan abubuwa ma’abota basira mai ruruwa mai tsananin haske abar haskakawa da fahimta sunawa mutane bushara da rabauta ta har abada, suna masu dogara ga dubban alƙawuranKa na alherai da alƙawarukanKa na narkon waɗandaka ambace su cikin maimaitawa da jaddadawa a cikin dukkan takardun da Ka saukar daga sama,da littattafai masu tsarki, kuma suna masu dogara da siffofinKa da sha’anoninKa na tsarkaka waɗanda suke wajabta samuwar Lahira,kamar ƙudura da jin ƙai da kulawa da hikima da jalala da jamala, kuma suna masu dogara bisa buwayar jalalarKa da sarautar ubangijintakarKa,kuma dogaro da kashafe-kashafensu da ganinsu marasa iyaka da suke nuni bisa guraban Lahira da tsattsafe-tsattsafenta, kuma dogaro da ƙudurcewarsu da imaninsu wanda ya kai matakin sani na yaƙini da ainihin yaƙini, kuma suna ba da labari suna shelantawa cewa akwai Jahannama ga ma’abota ɓata, da Aljanna ga ma’abota shiriya, kuma suna ba da gaskiya ba da gaskiya tabbatacciya,kuma suna shaidawa a kan haka shaidawa mai ƙarfi.

 


123. Page

Ya mai iko, ya mai hikima, ya mai rahama mai jin ƙai, ya mai gaskiyar alƙawari ya mai karamci, ya mabuwayi ma’abocin jalala ma’abocin buwaya da girma, haƙiƙa kai abin tsarkakewa ne da ɗaruruwan dubban darajoji, kuma abin tsarkakewa ne mai jin ɗaukaka ne, tsarkaka da ɗaukaka marasa iyaka ne ga barin ƙaryatawa ga wannan adadi na waliyyanKa masu gaskiya, da wannan adadi na alƙawarorinKa, da siffofinKa da sha’anoninKa, kuma daga ƙaryata abubuwa masu wajabtawa masu tabbatarwa ga sarautar ubangijintakarKa, da rashin tsayuwa da waɗannan abubuwa masu wajabtawar, kuma ga barin rashin jin addu’o’i da kiraye-kiraye marasa iyaka da ake fuskantar da su zuwa Lahira daga bayinKa karɓaɓɓu a wajanKa marasa iyaka, waɗanda kake son su kuma su a kan kansu suna ƙoƙarin soyantar da kawunansu zuwa gare ka, ta hanyar ba da gaskiya da Kai, da biyayya gare ka, kuma ga barin gasgata ma’abota ɓata da ma’abota kafirci waɗanda – ta hanyar kafirci da saɓo da ƙaryataKa cikin alƙawarinKa – suke taɓa girmanKa, kuma suke munanawa zuwa buwayar jalalarKa, suke taɓa buwayar AllahntakarKa, suke cutar da tausayin ubangijintakarKa, kuma ga barin tabbatarwar waɗannan cikin inkarin tashin Alƙiyama.

 

Muna tsarkake adalcinKa na sake babu ƙaidi, da kyawunKa na sake babu ƙaidi, da rahamarKa ta sake babu ƙaidi, tsarkakewa ta sake babu ƙaidi daga irin wannan zalunci na sake babu ƙaidi, da muni irin wannan na sake babu kaidi, kuma muna ba da gaskiya da dukkan ƙarfinmu cewa shaidar ɗaruruwan dubban manzanni masu gaskiya da annabawa da zaɓaɓɓu da waliyyai masu kira i zuwa masarautarKa masu gaskiya waɗanda ba za su ƙirgu ba, bisa matakin gaskiyar yaƙini da iliminsa da ainihinsa bisa taskokin rahamarKa ta Lahira, kuma bisa taskokin kyautayinKa a duniyar wanzuwa, da bisa tajallolin kyawawa masu ƙayatarwa na sunayenKa kyawawa waɗanda suke tajalli a gidan rabauta tajalli cikakke, da isharorinsu masu gaskiya da dacewa, da bisharorinsu, muna shaidawa cewa su gaskiya ne kuma masu afkuwa ne.

 

Kuma su suna ba da gaskiya cewa mafi girman haskakawa na sunan Al-Haƙƙuwato sarki na gaskiya-wanda shi ne makomar dukkan haƙiƙoƙi kuma shi ne 

124. Page

ranarsu kuma mai kiyaye su-shi ne haƙiƙar wannan tashin AlƘiyama mafi girma,kuma suna karantar da bayinKa wannan haƙiƙa da umarninKa cikin ƙunshin da’irar gaskiya, kuma suna sanar da su ita kamar ita ce ainihin haƙiƙar.

Ya Ubangiji, Ka azurta mu kuma ka azurta ɗaliban Rasa’il An-Nur da imani mafi cika, da kyakkyawar cikawa don haƙƙi da alfarmar darussa da koyarwar waɗancan, kuma ka azurta mu da cetonsu, amin.

 

Kuma kamar yadda dukkan dalilai da hujjojin da suke tabbatar da cancantuwar Alƙur’ani, koma cancatuwar dukkan littattafai saukakku daga sama, da dukkanin mu’ujizozi da hujjoji da suke tabbatar da annabcin masoyin Allah, koma annabcin dukkanin annabawa; suna nuni ne a lokaci guda bisa tabbatuwar Lahira wadda ita ce batunsu mafi girma; hakanan mafi yawancin dalilai da hujjoji waɗanda suke shaidawa bisa samuwar wanda samuwarsa take wajiba da kaɗaitakarsa, suna shaidawa a lokaci guda a kan samuwar da buɗuwar gidan rabauta da duniyar wanzuwa waɗanda su biyun su ne mafi girman abin da ubangijintaka da Allahntaka suke kewayawa a kansa kuma su ne mabayyanarsu.

 

Domin samuwar zati wanda samuwarSa wajiba ce da dukkan siffofinSa-kamar yadda zai bayyana kuma ya tabbata a cikin maƙamomi masu zuwa-da mafi yawancin sunayenSa da siffofinSa da sha’anoninSa kamar ubangijintaka da Allahntaka da jin ƙai da kulawa da hikima da adalci; dukkaninsu suna wajabta Lahira da matakin lazimtuwa, kuma suna lazimta samuwar wata duniya wanzajjiya da matakin wajabci, kuma suna buƙatar tashin Alƙiyama da ba za halittu a filin Alƙiyama domin yin kyakkyawan sakamako da uƙuba da matakin tilasta.


125. Page

Na’am, tun da daiAllah samamme ne tun fil azal kuma samamme ne har abada; to babu shakka cewa Lahira wadda ita ce gurin da masarautar AllahntakarSa ke kewayawa har abada samammiya ce.

 

Kuma tun da cewa lallai akwai ubangijintaka ta sake babu ƙaidi mai matuƙar girma da hikima da tausayi ana ganinta a wannan duniya kuma cikin ma’abota rayuwa, to babu kokwanto cewa za a samu wani gida na rabauta na har abadada za a kuɓutar da girman wannan ubangijintaka daga faɗuwa, kuma za a kuɓutar da hikimarta daga zama abin wasa, za a kuɓutar da tausayinta daga zama abin yaudara, kuma za a shiga wannan gida.

 

Kuma tun da nau’o’i marasa iyaka na ni’imtawa da kyautatawa da tausasawa da karamci da kulawa da jin ƙai da ake ganinsu da idanu suna nuna samuwar mai rahama mai jin ƙai ta bayan hijabin gaibi ga hankula waɗanda ba su bice ba, da zukatan da ba su mutu ba; to ba shakka wata rayuwa za ta zo wanzajjiya a duniya 

126. Page

wanzajjiya da za ta kuɓutar da ni’imtarwar daga izgili, ta kuɓutar da kyautatawar daga hilata, ta kuɓutar da kulawar daga adawa, ta kuɓutar da rahamar daga azaba,ta kuɓutar da tausasawar da karamcin daga wulaƙantawa,kuma ta sanya kyautatawar ta zama kyautatawa ta haƙiƙa, kuma ta sanya ni’imar ta zama ni’ima ta haƙiƙa.

 

Kuma tundacewa alƙalami na ƙudura ya rubuta littafi dubu ɗari masu shiga juna ba tare da kuskure ba a lokacin kaka a cikin shafi mai ƙunci na doron ƙasa, yana aiki a gaban idanunmu ba tare da gajiyawa ba, kuma tun da cewa ma’abocin wannan alƙalami ya ci alwashi kuma ya yi alƙawari sau dubu ɗari, kuma ya ce haƙiƙa ni zan rubuta muku littafi mai ban sha’awa madawwami a wani guri mai yalwa ta hanya mafi sauƙi daga littafin lokacin kaka wanda aka rubuta cikin cakuɗa da shiga juna a cikin wannan guri ƙuntatacce kuma zan karanta muku shi, kuma yana magana game da wannan littafi a cikin duk dokokinSa; to babu shakka kuma babu makawa cewa asalin wannan littafi an riga an rubuta shi, kuma da sannu za a rubuta rubututtukan hamisoshinsa da hashiyoyinsa ta hanyar tashin matattu da korasu zuwa filin Alƙiyama, kuma da sannu za a rubuta takardun dukkan ayyukan kowa da kowa a cikinsa.

 

Kuma tun da cewa wannan ƙasar ta fuskar yawan ababan halitta da ke cikinta, da ta fuskar kasancewarta ita ce mazaunar ɗaruruwan dubban nau’i-nau’i na ma’abota rayuwa da ma’abota rayuka masu sabunta ko da yaushe, kuma ita ce masomarsu kuma masamarsu kuma mashahararsu kuma matasarsu, kuma ita ce zuciyar halitta kuma cibiyarta kuma ƙunarinta kuma sakamakonta kuma sababin halittarta; don haka haƙiƙa tana da muhimmanci babba, ta yadda ita duk da ƙanƙantarta an sanya ta daura da waɗannan sammai gingima-gingima, don haka ko yaushe a ke cewa a cikin dokoki na sammaiرَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ[1]


[1]{Ubangijin sammai da ƙasa}[Sad:66].

 




127. Page

Kuma tun da cewa akwai wani nau’i na ɗan’adam da yake mulkin dukkan geffan ƙasa wadda ta ke da irin wannan haƙiƙa, kuma yake tasarrufi a cikin mafi yawan ababan halittarta, kuma yake hore mafi yawan samammun abubuwan da ke cikinta ma’abota rayuwa, kuma yake sanyasu su taru su kewaye shi, kuma yake tsara mafi yawan ababan samarwarta, kuma ya bijiro da su ya ƙawata su, cikin matuƙar ban sha’awa da kyawu da surantawa ta son ransa da burinsa da tsare-tsaren buƙatunsa, kuma yana tattara nau’o’insu waɗanda su kayan tarihi ne masu matuƙar ƙaranci ƙwarai a wasu guraren kamar ka ce shi yana tsara su ne a wani jerin sunaye kuma ya ƙawata su, ta yadda shi yake samun muhimmanci da ƙima masu girma ƙwarai, ba wai da janyo hankalin mutane da aljanu ba kawai,har ma da jawo hankali da kuma samun ganin daraja daga ma’abotan sammai da ma wannan halitta gaba 

128. Page

ɗaya, dama janyo kallo na ganin kyawu daga ma’abocin wannan halitta, ta wannan hanya ne yake bayyana ta hanyar ilimansa da fasahohinsa a matsayin cewa shi ne hikimar halittar wannan samuwa, kuma sakamakonta mafi girma, kuma ɗan itaciyarta mai ƙima, kuma cewa shi halifan bayan ƙasa ne, kuma zai wanzu a duniya kuma a jinkirta azabarsa duk da saɓonsa da kafircinsa; domin shi ta mahanga ta duniya yana bijiro da kuma tsara ƙere-ƙere na mai samar da wannan duniya ma’abociyar mu’ujizozi bijirowa da tsarawa mai ban sha’awa, kuma ana masa jinkiri domin wannan hidima da yake, sai a yi masa gam da katar.

 

Kuma tun da cewa akwai wani mai tasarrufi ma’abocin iko da hikima da tausayi na sake babu ƙaidi da ya sanya ƙwallon duniya babba ga bani Adama sama da ƙarfinsu da zaɓinsu gaba ɗaya kuma wannan ita ce haƙiƙaninsu,kuma tare da cewa shi rarrauna ne kuma gajiyayye ne ƙwarai ta ɓangaren zubin halittarsa da halittar tasa, kuma yana da buƙatu da jin raɗaɗi da ba su da iyaka tare da matuƙar gazawar sa da buƙatuwarsa..Na ce haƙiƙa shi Mahalicci ya sanya Ƙwallon duniya babba kamar wata ma’ajiya ce ta dukkan wani nau’i na nau’o’in ma’adanai da kowane mutum ke matuƙar buƙatarsu, kuma ya sanya shi wata ma’ajiya ta kowane nau’i na nau’o’in abinci, kuma wani kanti ne da yake ƙunshe da kowane nau’i daga nau’o’in hajojin da kowane mutum ke marmari,irin haka shi yake tattalin dangin ‘yan’dam, kuma yake ciyar da su yake ba su abin da suke so.


129. Page

Kuma tun da ubangijin da yake da wannan haƙiƙa ya na son mutum, kuma yake yi wa ɗan’adam abin da zai sa ya so shi, kuma cewa shi wanzajje ne, kuma yana da duniyoyi wanzazzu, kuma yana aikata kowane abu da adalci, kuma dukkan ayyuka-yana yinsu- da hikima, kuma cewa wannan rayuwa ta duniya ‘yar gajeriya, kuma rayuwar bil Adama gajeriya ce ƙwarai, kuma wannan duniyar ta ɗan lokaci ƙararriya ba za ta wadaci girman masarautar wancan mai sarautar na tun fil azal ba,da kuma sarmadiyyar masarautakarsa, kuma cewa zalunci da ayyukan saɓo manya-manya da jinsin ‘yan’dam suke aikatawa, waɗanda suke karo kuma suke saɓawa da tsaruwar halitta da adalcinta da daidaituwarta da kyawun kyanta, da ƙasƙantawar mutum da inkarinsa da kafircewarsa ga majiɓincin ni’imarsa, ga kuma wanda yake azurta shi da tausayinsa, duk wannan ya wanzu ba tare da uƙuba a cikin wannan duniya ba, sai azzalumi mai danniya ya ƙare rayuwarsa cikin sakewa, kuma wanda aka zalunta miskini ya ƙare rayuwarsa cikin wahalhalu, sai dai haƙiƙanin adalci na sake babu ƙaidi wanda a ke ganin gurabansa a cikin dukkan halitta, yana cin karo baki ɗaya ga daidaita azzalumai masu danniya da waɗanda aka zalunta masu ɗebe ƙauna cikin mutuwar da babu wani tashi bayanta, kuma ba zai ɗauki yiwuwar hakan ba ko ba da damar aukuwarsa.

 


130. Page

Kuma tun da cewa ma’abocin halitta ya zaɓi ƙasa daga cikin halitta, kuma ya zaɓi nau’in ɗan’adam daga ƙasa, ya ba shi muƙami mai girma,ya jiɓinta masa muhimmanci mai girma ƙwarai, to hakanan ya zaɓi annabawa da waliyyai da zaɓabbun bayi waɗanda su su ne mutane na haƙiƙa a tsakankanin jinsin ɗan’adam, kuma waɗanda suke dacewa tare da muradun ubangijintakarSa, kuma sukeyin abin da za su sanya soyayyarsu a wajanSa ta hanyar imani da miƙa wuya, sai ya sanya su majiɓinta kuma ababan yin magana da Shi, kuma ya girmama su da mu’ujizozi da gam da katar, kuma yake azabtar da abokan gabarsu da wasu azabobi saukakku daga sama, kuma daga cikin majiɓintanSa waliyyanSa masu girma masoya ya zaɓi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda shi ne shugabansu kuma alfaharinsu, kuma ya haskaka da haskensa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-cikin ƙarnoni masu tsawo, rabin ƙwallon duniya mai muhimmanci, da ɗaya bisa biyar na dangin ɗan’adam mai muhimmanci, domin dukkan muradu suna bayyana ne da shi da addininsa da Alƙur’aninsa, kamar ka ce dai halitta an halicce ta ne domin shi kansa, kuma ga shi an ba shi rayuwa gajeriya cikin wahalhalu da ƙoƙari mai wahalar gaske, kuma ya ƙaddara ta tsawon shekara sittin da uku, tare da cewa shi ya cancanci ya karɓi ladan hidimarsa mai tsada mara iyaka da gwargwadon miliyoyin shekaru a lokaci mara iyaka.

 


131. Page

To ya jama’a! Shin akwai wata iyawa ko wata yiwuwa ta kowace fuska na cewa ba za a tashi wannan manzo-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-tare da makamantansa da masoyansa ba?Kuma a ce shi a yanzu ba rayayye ba ne mai siffar ruhi?Kuma a ce shi zai ƙare shi da makamantansa da rasuwa ta har abada?Allah ya kiyaye sau dubu, faufau kuma a’a.

 

Na’am, haƙiƙa dukkan halitta da haƙiƙar wannan duniyar suna neman tada shi, kuma suna nema daga mamallakin halitta cewa ya rayu.

 

Kuma tun da haƙiƙa cewa shi ya tabbatar da ijima’i talatin da uku masu girma-kowane ɗaya daga cikinsu ya kai ƙarfin dutse-cikin Risalar”Al-Aya Al-Kubra”-Aya mafi girma- wadda ita ce “Haskakawa ta bakwai”, cewa wannan halitta ta samo tushe ne daga hannu guda ɗaya, kuma cewa ita mallaka ce ta wanda yake Shi ɗaya ne, kuma ya bayyana kaɗaitaka da ɗayantaka ta Allah mai cikakken ƙarfi waɗanda a kansu ne kamalolinSa ke gewayawa,kai ka ce yadda kowa ya sanikamar dai halitta za ta zama ƙarfi ne na wannan makaɗaicin da ikonsa ta hanyar kaɗaitakar da ɗayantakar, kuma dukkan ababan halitta za su zama runduna ce mai aiwatar da umarninSa, kuma ma’aikata ne ababan ba umarni kuma ababan horewa ga wannan makaɗaicin mai tsarki da ɗaukaka, kuma cewa da zuwan Lahira kamalolinSa za su tsira daga saraya, kuma adalcinSa na sake babu ƙaidi zai kuɓuta daga zalunci cikakke cikin izgili, kuma hikimarSa magamiya za ta kuɓuta daga 

132. Page

kasancewa abar yi don wasa cikin wauta, kuma rahamarSa mayalwaciya za ta kuɓuta daga azabtarwa cikin wargi, kuma buwayar ikonSa za ta kuɓuta daga gajiyawa cikin ƙasƙanci, kuma dukkaninsu za su tsarkaka; don haka ba shakka kuma babu kokwanto cewa Alƙiyama za ta tsaya, da wajabtawar abubuwan da aka ambata cikin “Kuma tunda” guda takwas cikin ɗaruruwan sirrorin hikima na imani da Allah, kuma tashin mutane da kora su zuwa filin Alƙiyama zai faru, kuma za a buɗe gidan uƙuba da gidan kyakkyawan sakamako don muhimmancin ƙasa da kasancewarta mafi muhimmanci da aka ambata ya tabbata, da kuma muhimmancin ɗan’adam da ƙimarsa, kuma adalci da hikima da jin ƙai da sarauta da ka ambata na Mai tasrifi Mai hikima Mahaliccin ƙasa da mutum kuma ubangijinsu su tabbata, kuma waliyyan wancan ubangiji wanzajje da masu shauƙi zuwa gare shi da aka ambata na haƙiƙa su kuɓuta daga rasarwa ta har abada, kuma mafi girman waɗancan waliyyan kuma mafi muhimmancinsu su sami kyakkyawan sakamako na hidimta maSa wadda za ta yardar da dukkan halitta, kuma ta sanya su su zama masu godiya masu yaba baiwa, kuma kamalolin sarki na har abada su tsarkaka su kuɓuta daga tawaya da kasawa, kuma ƙudurarSa ta tsarkaka daga gazawa, kuma hikimarSa ta tsarkaka daga wauta, kuma adalicinsa ya kuɓuta daga zalunci.

 

A ƙarshe dai:Tun da Allah yana nan; to babu kokwanto cewa Lahira samammiya ce.

 

Kuma kamar yadda rukunan imani guda uku da aka ambata suke shaidawa bisa tashin Alƙiyama, kuma suke nuni zuwa gare shi da dukkanin dalilansu da suke tabbatar da su; hakanan rukunai biyu na imani wanɗanda su ne “da mala’ikunSa da ƙaddara ta alherinta ko kishiyar hakan cewa daga Allah Ta’ala suke”suna wajabta tashin Alƙiyama kuma suna nuni bisa duniyar wanzuwa da ƙarfin samuwarsu, kamar haka:

 


133. Page

Haƙiƙa dukkan dalilai da abubuwan da ake gani da zantuttukan da ake musayarsu marasa iyaka da suke tabbatar da samuwar mala’iku da aikin bautatuwarsu, suna nuni hakanan ma bisa samuwar duniyar rayuka da duniyar gaibu da duniyar wanzuwa da duniyar Lahira da gidan rabauta waɗandamutane da aljanu za a rayar da su a cikinta nan gaba, da kuma samuwar aljanna da wuta; domin mala’iku za su iya ganin waɗannan duniyoyi da izinin ubangijintaka kuma su shigesu, kuma dukkan mala’iku ababan kusantawa waɗanda suke gamuwa da mutane kamar Jabra’ilu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suna ba da labari bisa haɗuwar maganarsu game da samuwar waɗannan duniyoyi da aka ambata, kuma cewa su suna kewayawa a cikin waɗancan duniyoyi, kuma kamar yadda yake abu ne da kowannenmu ya sani cewa akwai Nahiyar Amurka wadda ba mu ganta ba ta hanyar ba da labarin waɗanda suke zuwa daga gare ta, hakanan ya wajaba a yi 

134. Page

imani-a matakin irin wancan na yanke shakku-da samuwar duniyar wanzuwa da gidan Lahira, da aljanna da wuta ta hanyar ba da labarin mala’iku wanda ya kai ƙarfin matakin ruwan dare gama duniya sau ɗari, to haka muke ba da gaskiya.

 

Sannan dukkan dalilai da suke tabbatar da rukunin imani(imani da ƙaddara) na“Risalatul Ƙadar”[1] wadda ita ce “Kalma ta ashirin da shida”, suna nuni hakanan ga tashin ƙiyama da yaɗa takardu da auna ayyuka a ma’auni mafi girma; domin rubuce da adana gwargwadon kowane abu a gaban idonmu a allon tsari da ma’auni, da rubuta dukkan abin da ya faru a rayuwar kowane abu mai rai a ƙwaƙwalwarsu da ƙwallon halittarsu, da kuma cikin ragowar alluna na samfuri, da rubuce littafin ayyukan duk wani abu mai rai-musamman ma mutum-da tabbatar da shi a alluna ababan kiyayewa; babu shakka cewa wani gwargwado irin wannan, da gwargwajewa mai hikima da ƙayyadewa mai bin ƙwaƙƙwafi da rubutu mai kiyayewa; duk wannan ba zai yiwu ya faru ba face sai dai saboda kyakkyawan sakamako da sakawa madawwamiya bayan yin hukunci magami a babbar kotu, in ba haka ba sai rubucewar mai kewayewa da waccan kiyayewar su zama ba su da ma’ana ko fa’ida, kuma ya kasance mai cin karo gaba ɗaya da hikima da haƙiƙa, kuma idan tashin Alƙiyama bai auku ba da ma’anonin dukkan littafin wannan halitta da aka rubuta da Alƙalamin ƙaddara sun ɓaci; kenan hakan ba za ta yiwu ba ta kowace fuska.


[1](Risalar imani da ƙaddara) 




135. Page

Wannan hasashen ba mai yiwuwa ba ne, maimakon haka ma shi tamɓele ne kamar dai inkarin samuwar wannan halitta.

 

A ƙarshe dai:Haƙiƙa rukunan imani guda biyar suna nuni da dukkan dalilansu bisa samuwar tashin alƙiyama da kora mutane zuwa filin Alƙiyama, da aukuwarsu da samuwar gidan Lahira da buɗewarsa, kuma suna buƙatarsu, kuma suna shaidawa kuma suna nemansu.

 

Kuma tun da wannan haƙiƙar tashin Alƙiyamar tana da ginshiƙai da hujjoji manya-manya da ba za su raurawa ba, kuma suna dacewa cikakkiyar dacewa da girman tashin Alƙiyamar, to haƙiƙar sulusin Alƙur’ani mai bayani mai gajiyarwa kusan ya ƙunshi lamarin tashin Alƙiyama da Lahira ne, kuma yana sanya su a matsayin tubali na haƙiƙoƙinsa, kuma tushen tuwasunsa, kuma yana gina kowane abu ne a kansu.

(Muƙaddimar ta ƙare)