Nuƙuɗa ta Farko

114. Page

bayyana ƙarara ƙarfafa ƙwarai ga ɗaya daga cikin waɗannan ayoyi biyu dokar ubangiji da tafsirorinta wadda ita ce

فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡض بَعۡدَمَوۡتِهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِير


Kuma ya yi mini ni’ima bayan shekaru tara ko goma daga waɗannan sansanoni biyu masu ƙarfiƙwarai na aƙidar tashin Alƙiyama, da wallafa wannan risala a matsayin tafsiri na ayoyi manya-manya da aka ambata a baya, wadda ita ce aya ta biyu.

 Wannan haske na tara yana matsayin maƙamomi ne guda tara maɗaukaka da gabatarwa muhimmiya da a ke yin nuni zuwa gare su a cikin ayoyin da aka ambata.

 

Gabatarwa: Nuƙuɗoɗi biyu da suke a matsayin bayani na fa’idoji na ruhi masu yawa ƙwarai ga aƙidar tashin AlƘiyama, kuma sakamako ne matattari na sakamakonta na rayuwa a taƙaice, da bayyana irin zurfin kasancewarta lalura,da kuma lazimtarta ga rayuwar bil Adama musamman ma rayuwarsa ta zamantakewa, da kuma fayyacewa game da hujja matattariya tsakanin hujjojin aƙidar imani da tashin AlƘiyama masu yawa ƙwarai a dunƙule, da fa’idantar da yadda cewa wannan aƙidar abu ne da kowa ya sani babu shakka.

 

Nuƙuɗa ta Farko: Za mu yi nuni zuwa dalilai huɗu-A matsayin magwadai-a tsakanin ɗaruruwan dalilai da suke nuni cewa haƙiƙa aƙidar Lahira ita ce tushen rayuwa ta zamantakewa da rayuwa ta mutum a kan kansa, kuma cewa ita ce tuwasun rabautarsa da kamalolinsa.

 

Dalili na Farko: Yara waɗanda su ne kusan rabin ‘yan’dam ba za su iya jurewa ba a gaban mace-mace ko mutuwa ba wadda ta ke ɓuɓɓulo musu a matsayin abu mai razanarwa da sa kuka sai da tunanin Aljanna, kuma da wannan tunani za su iya samun ƙarfi na ma’ana a cikin zatinsu mai rauni tattausa ƙwarai,kuma za su iya samun buri da fata da tunanin Aljanna a cikin yanayin ruhinsu rarrauna ƙwarai, kuma mai saurin kuka daga kowane abu mai tasiri, wannan sai ya ba su damar rayuwa cikin farin ciki da sakin rai.

 

Ga misali:Da tunanin Aljanna zai ce: ɗan’uwana ƙarami ko abokina ya rasu, sai ya zama tsuntsu daga tsuntsayen Aljanna, yana kewayawa a cikinta yana rayuwa yana morewa da jin daɗi fiye da mu, in ba haka ba sai mutuwar sakonsa daga yara da ma manya da ke tare da su ta zama abu ne da zai ɗimauta idanun waɗannan miskinan raunana waɗanda ba sa tsayawa guri ɗaya, kuma ta ruguza juriyarsu da ƙarfinsu na ma’ana, kuma bayan idanunsu ma za ta sanya ɓoyayyaun abubuwansu kuka, kamar ruhinsu da zuciyarsu da hankulansu, sai ya zama ko dai su tozarta, ko kuma su zama kamar dabbobi masu shiga uku da wahala da gararamba.


115. Page

Dalili na Biyu:Tsofaffi maza da mata waɗanda su -ta wata fuskar-su ne rabin ‘yan’dam da tunanin rayuwar Lahira ne kawai za su iya jurewa ga fuskantar ƙabari da yake a dab da su,kuma su iya samun sa’ida a madadin bicewar rayuwarsu da suka ɗamfaru suka shaƙu da ita ƙwarai nan ba da jimawa ba, kuma a madadin rufewar da duniyarsu kyakkyawa za ta yi, kuma da burin rayuwa wanzajjiya kawai ne za su iya jurewa a gaban tsanani mai ɗaci mai razanarwa da ke zuwa daga mutuwa da gushewar rayukansu da ɗabi’arsu mai tsananin ji da sosuwa, wadda ta zama kamar ta yara ita ma tana saurin tasirantuwa.

In ba don haka ba, da waɗannan masu daraja ababan girmamawa da suka cancanci tausayawa, da iyaye maza da mata masu rashin nutsuwa da damuwa waɗanda suke matuƙar buƙatar nutsuwa da hutun zuciya, da sun ji kururuwar ruhi da baƙƙan ciki na zuciya, da za su sanya wannan duniyar ta zama ɗakin kurkuku gare su, kuma rayuwa ta zama azaba mai tsauri gare su.

 

Dalili na Uku: Samari da ‘Yan mata su ne mafi ƙarfin abin dogaro a rayuwar zamantakewar ‘yan’dam, kuma abin da kawai ke dakatar da abubuwan da suke ji a ransu masu ƙarfi, da zuciyoyinsu da soye-soyen zuciyarsu masu wuce gona da iri da zalunci da ruguza abubuwa, kuma abin da zai sanya rayuwar zamantakewa ta tafi a magudanarta ta ɗabi’a shi ne tuna Jahannama,da ba don akwai tsoron Jahannama ba; da waɗannan matasa masu tamɓele masu gudu suna bin soye-soyen zukatansu da kwaɗaye-kwaɗayensu, da sun maida duniya wata Jahannamar ga raunana miskinai gajiyayyu daidai da ƙa’idar “Hukunci na mai rinjaye ne”,da kuma sun mai da mutumtaka maɗaukakiya zuwa dabbantaka cikin matuƙar ƙasƙanta.


116. Page

Dalili na Huɗu: Haƙiƙa matattara mafi yawan tattarawa kuma mafara mafi ƙarfin tushe, kuma aljanna da mafaka da matserata ga rabauta da farin ciki na duniya ga dangin ɗan’adam; shi ne rayuwar iyali, kuma gidan kowane mutum ɗaya duniya ce ƙarama, kuma rayuwar wannan gida da rayuwar wannan iyali da farin cikinsu suna samuwa ne da tsantsar girmamawa tuƙuru cikin riƙe alƙawari, da kuma jin ƙai na haƙiƙa ma’abocin tausasawa cikin sadaukarwa, kuma wannan tsantsar girmamawa da jin ƙai na gaske suna samuwa ne ta hanyar abota ta har abada da tausasawa madawwamiya da tarayya ta har abada da aƙida da tunani-cikin lokaci mara ƙarewa, da rayuwa mara iyaka-cikin samuwar wasu lokutan wasu abubuwa na musamman a tsakaninsu wanda ubantaka da ɗiyantaka da ‘yan’uwantaka da abokantaka suka cika su.

 

Ga misali yana cewa: Haƙiƙa matata wannan ita ce abokiyar rayuwata madawwamiya a wata duniya ta har abada kuma cikin rayuwa ta dindindin, kuma ba laifi in ta zama tsohuwa kuma mummuna yanzu, domin tana da wani kyawu na har abada da zai zo.


117. Page

Kuma wasu amfane-amfanen daban za su yi rinjaye da sauran abubuwan da ake ji a jiki marinjaya-kamar yadda yake a wajen dabbobi-za su yi rinjaye a kan waccan girmamawa da wancan jin ƙan, kuma su mai da waccan aljannar ta duniya zuwa Jahimu.

 

Don haka sakamako ɗaya daga ɗaruruwan sakamako na imani da tashin Alƙiyama yana rataye ne da rayuwar mutum ta zamantakewa, kuma idan aka ƙiyasta wasu sakamakon daga ɗaruruwan fuskoki da fa’idojin wannan sakamako ɗaya da waɗannan hujjoji guda huɗu to za a fahimci cewa haƙiƙar tashin Alƙiyama da faruwarsa abu ne tabbas da ta kai matakin tabbacin haƙiƙa maɗaukakiya mai daraja ga ‘yan’adamtaka da buƙatunta matattara.koma a ce ita-haƙiƙar tashin Alƙiyamar-ta fi bayyana daga shaida da manuniyar samuwar buƙatuwa a cikin tumbin mutum bisa samuwar abinci, kuma suna ba da labari game da samuwarta ba da labari mafi ƙarfi da tsanani.

 

Kuma suna tabbatar da cewa da waɗannan sakamako na wannan haƙiƙa ta tashin Alƙiyama sun tsaraita daga ma’anar ‘yan’damtaka da haƙiƙar ɗan’adam wadda ita mai matuƙar muhimmanci ce da ɗaukaka kuma cike suke da rayuwa, da ta saraya zuwa matsayin mushe mai ruɓewa da zai zama gurin dabdala da kiwo na ƙwayoyin cuta.

 

To lallai wannan ya yi ƙararrawa a kunnuwan masu kula da zamantakewa da ‘yan siyasa da masu damuwa da halayya waɗanda suke damuwa matuƙa da gudanar da harkokin ‘yan’dam da halayensu da zamantakewarsu! Su gaya mana da me za su iya cika wannan giɓin, kuma da me za su iya magance waɗannan raunuka masu zurfi?